An rantsar da Shugaba Assad wa’adin mulki karo na uku

A shekaranjiya Laraba ne aka gudanar da bikin rantsar da Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad wa’adin zangon mulki karo na uku bayan samun nasararsa a zaben da ’yan adawar kasar suka bayyana da “wasan yara”.Shugaba Assad ya daukin rantsuwar kama mulki ne rike da al- kur’ani Mai Girma a gaban ’yan majalisar dokokin kasar, a […]

An rantsar da Shugaba Assad wa’adin mulki karo na uku
An rantsar da Shugaba Assad wa’adin mulki karo na uku

A shekaranjiya Laraba ne aka gudanar da bikin rantsar da Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad wa’adin zangon mulki karo na uku bayan samun nasararsa a zaben da ’yan adawar kasar suka bayyana da “wasan yara”.
Shugaba Assad ya daukin rantsuwar kama mulki ne rike da al- kur’ani Mai Girma a gaban ’yan majalisar dokokin kasar, a wani abu da ba a saba gani ba kimanin watanni 40 bayan fara yakin basasar kasar wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum dubu 100.
A jawabin rantsarwan, shugaban ya suke lamirin kasashen Yamma da wasu daga cikin kasashen Larabawa, ya kuma ce guguwar sauyin da ta kada a kasashen Larabawan ba ta kawo komai ba, ban da tashin hankali.
“Abun da muke gani yanzu a kasashen Iraki da Lebanon da sauran kasashen da wannan annobar guguwar sauyin karyar ta ratsa, sun tabbatar da irin gargadin da muka yi. Amma nan gaba kadan, kasashen Larabawa da Yammacin Duniya za su  ga mummunar sakamakon ayyukansu na taimakawa ta’addanci.” Inji shi.
Shugaba Assad ya samu nasara ne a zaben shugaban kasar da aka gudanar a farkon watan jiya da kashi 88.7 cikin 100.