An rantsar da shugaban Kamaru Paul Biya karo na 8
Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba
An rantsar da Paul Biya a matsayin shugaban ƙasar Kamaru karo na takwas mai shekaru 93 a majalisar dokokin ƙasar da ke Yaoundé.
Paul Biya ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, kuma yanzu zai fara wani wa’adi na tsawon shekara bakwai nan gaba.
- Ƙungiyyar Ƙwallon yashi ta Kada BSC ta fatattaki Kebbi BSC
- Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
Biya wanda shine shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya, ya sami kashi 54 na ƙuri’un zaɓe, yayin da abokin takararsa, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35%, a cewar sakamakon zaɓen hukumar ƙasa.
Tchiroma Bakary dai ya yi iƙirarin cin nasara a zaɓen da aka yi yana kuma zargin cewa an yi maguɗin zabe, wanda hukumomi suka musanta.