An rantsar da shugabannin kungiyar nakasassu ta Jami’ar Jihar Nasarawa

A kwanakin baya ne kungiyar dalibai nakasassu ta Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi ta yi taron yaye mambobinta tare da rantsar da sabbi domin ci gaba da gudanar da ayyukan kungiyar kamar yadda ya dace. An gudanar da taron ne a cikin jami’ar, inda aka rantsar da Idris Muhammad a matsayin sabon shugaban […]

An rantsar da shugabannin kungiyar nakasassu ta Jami’ar Jihar Nasarawa
An rantsar da shugabannin kungiyar nakasassu ta Jami’ar Jihar Nasarawa

A kwanakin baya ne kungiyar dalibai nakasassu ta Jami’ar Jihar Nasarawa da ke garin Keffi ta yi taron yaye mambobinta tare da rantsar da sabbi domin ci gaba da gudanar da ayyukan kungiyar kamar yadda ya dace.

An gudanar da taron ne a cikin jami’ar, inda aka rantsar da Idris Muhammad a matsayin sabon shugaban kungiyar, sai kuma Abisabo Abdullahi a matsayin sabon babban sakataren kungiyar. Har ila yau, akwai Ibrahim Umar Faransa a matsayin sabon sakataren kudin kungiyar, sai Yusuf D. Yusuf a matsayin sabon ma’ajin kungiyar, sai kuma Ishimail Umar Abe a matsayin jami’in yada labaran kungiyar.
A jawabin Shugaban kungiyar Mai Barin Gado, Adams Nicholas, ya ce: “Nakasassu a kasar nan masamman a yankin Arewacin suna fuskanta matsaloli daban-daban kamarsu rashin samun tallafi daga al’umma, rashin ababan hawa da kuma, wariyar da ake nuna musu, wadannan su ne kadan daga cikin kalubalen da nakasassu ke fuskanta a Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi har da Najeriya baki daya.”
Adams ya ce shekarunsa biyu ke nan yana rike da mukamin a kungiyar, inda yayi shekara guda a matsayin sakatare sa’annan shekara guda kuma a kujerar shugaban kungiya.
Daga nan ya koka da da cewa, “duk iya kokarin da na yi na ganin an samar da sashin koyar da nakasassu na musamam kamarsu makafi da kuramai a jami’an nan, abin yaci tura,” inji shi.
Ana shi bangaren Ibrahim Sunday Ogwole, wanda shi ne tsohon ma’ajin kungiyar mai barin gado, ya ce babu shakka nakasassu musamman makafi suna fuskantar matsaloli da dama a jami’ar, musaman game da abinda ya shafi kayayyakin karatunsu.
Daga akarshe Ogwole ya yi kira ga gwamnatin Jihar Nasarawa da ta taimaka wa nakasassu, “domin nuna masu cewa suma suna da gata kamar kowanne mutum,” inji shi.