An rantsar da shugabannin NURTW na Katsina
An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), reshen Jihar Katsina, bayan zaben shugabannin kungiyar sakamakon kare wa’adin wadanda suka jagoranci kungiyar na tsawon shekara hudu sau biyu. Zaben ya gudana da samun daidaito a tsakanin ’yan takaran da suka fito daga shiyyoyi biyu a kan neman kujerar shugaba. Shiyyar Katsina ta fito […]
An rantsar da sababbin shugabannin Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW), reshen Jihar Katsina, bayan zaben shugabannin kungiyar sakamakon kare wa’adin wadanda suka jagoranci kungiyar na tsawon shekara hudu sau biyu.
Zaben ya gudana da samun daidaito a tsakanin ’yan takaran da suka fito daga shiyyoyi biyu a kan neman kujerar shugaba.
Shiyyar Katsina ta fito da ’yan takara hudu yayin da shiyyar Daura ta fito da mutum daya tak. Mutanen hudu da suka fito a shiyyar Katsina sun hada da Alhaji Jamilu Shu’aibu da Alhaji Lawal Gwaram da Alhaji Garba Ramso sai Alhaji Mainasara Jibiya, yayin da Alhaji Musa ’Yandoma ya fito daga shiyyar Daura.
A jawabins Shugaban Kungiyar da ya bari gado, Alhaji Sajen Haruna Muhammad ya ce, kungiyar ta yanke shawarar kawo taron cikin babban birnin jihar ne domin nuna jin dadinta kan irin yadda Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi kokarin samar da zaman lafiya tare da kawo saukin hare-haren ’yan bindiga da masu satar shanu da yin garkuwa da mutane cikin jihar, inda ya ce samar da hakan ba karamin abu ba ne, domin ya sanya jama’a sun ci gaba da walwala tare da gudanar da harkokinsu na yau da kullum bayan ci gaba da harkokin sufuri cikin jihar ba tare da wata fargaba ba.
“Wannan kungiya na alfahari da irin gudunmawar da kake ba ta. Domin tun kirkiro Jihar Katsina kimanin shekara 32 ba a samu Gwamnan da ya bai wa wannan kungiyar bashin motoci har 84 sai kai. Kuma za a biya cikin wata 42 bisa farashi mai sauki. Wannan taimako kungiya na alfahari da shi sosai,” inji shi.
Ya kara da cewa: “Kazalika, muna sane da irin yadda kake kara inganta harkokin sufuri a cikin jihar wajen gina sababbin hanyoyin birane da karkara tare da gyara wadanda suka lalace. Ba sai mun ce ba, kowa ya ga irin yadda ka inganta harkokin noma da kiwon lafiya da ruwan sha da harkokin ilimi, mayar da wadansu ’yan SPower zuwa cikakkun ma’aikata ya tabbatar da haka.”
Sai ya sake tunatar da Gwamna Masari batun filin da za a gina babban ofishin kungiyar kasancewar wanda take da shi ya yi kadan lura da irin yadda kullum ake samun ci gaba a kungiyar.
Da yake mayar da jawabi, Gwamna Masari, wanda ya samu wakilcin Mai Ba shi Shawara kan Harkokin ’Yan Kwadago da Kyautatuwar Aiki Alhaji Tanimu Lawal Saulawa, wanda kuma tsohon shugaban kungiyar kwadago ne na jihar, ya fara da tuna irin yadda ya yi aiki da kungiyar na tsawon shekara hudu kan irin jajircewar kungiyar da ’ya’yanta wajen ganin sun cimma duk wani burin da suka sa gaba.
“Ina amfani da wannan dama a matsayina na wakilin Gwamna in yi kira ga sababbin shugabannin da za ku jagoranci kungiyar kan ku yi koyi da wadanda suka sauka domin ganin kun ciyar da kungiyar gaba. Ku bai wa gwamnati hadin kai tare da goyon baya domin samun ciyar da jihar da al’ummarta gaba. Sannan ina sanar da shugaba mai barin gado da sauran ’ya’yan wannan kungiya cewa, wannan koke ko tunatarwa da suka yi game da batun fili tamkar a cikin kunnuwan Gwamna suka yi shi. Ina da yakinin Gwamna zai ji kuma ya share muku hawaye don yana sane da irin gudunmawar da kuke ba gwamnati a fannoni daban-daban,” inji shi.
Bayan rantsuwar kama aiki da sababbin shugabannin suka yi ta hannun Barista Sadrack, sabon Shugaban wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar a shekara takwas, Alhaji Musa Garba ’Yandoma ya tabbatar wa ’ya’yan kungiyar cewa ba zai ba su kunya ba bisa wannan matsayi da suka dora masa.
“Hakika, wannan kungiya na son ci gaba sosai a zamanance wanda in Allah Ya so za mu yi iya kokarinmu don ganin an samu sababbin canje-canje masu ma’ana a kungiyar. Amma hakan ba zai samu ba sai tare da goyon bayanku da hadin kai,” inji shi.
Tun farko sai da Shugaban Ma’aikata na Jihar Katsina, Alhaji Idris Tune da wakilin Daraktan Kula da Lafiyar Motoci, (BIO), Alhaji Aminu Hamisu da Wakilin Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa na Jihar Katsina Abdullahi Maikano da na Hukumar Sibil Difens Hassan Muhammad Ruma suka gabatar da jawabai daban-dabam.
Shi ma Dankafin Katsina Alhaji Musa Adamu Funtuwa da Magaji ’Yandoma Alhaji Abubakar Ilyasu wanda ya wakilci Uban Doman Katsina, Alhaji Rabe Chake da sauran mutanen da aka gayyata sun tofa albarkacin bakinsu inda suka bayar da shawarwari tare da jan hankali game da nauyin da ke bisa kansu da yadda za su sauke kamar yadda magabatansu suka yi.
Shugabannin da aka zaba sun hada da Alhaji Musa Garba ’Yandoma a matsayin Shugaba da Shamsuddeen Sani, Mataimakin Shugaba da Dikko Abdulkadir, Mataimakin Babban Sakatare, Alhaji Ibrahim Muhammed Sheme Ma’aji, yayin da Sakataren Kudi ya shiga hannun Alhaji Tasi’u Musa.
Hassan Bakori ne Sakataren Shirye-Shirye yayin da Alhaji Lawal Hamisu ya zama Mai Binciken Kudi da sauran mukamai daban-daban.