An rantsar da shugabannin ’yan kasuwa na kananan hukumomin Jihar Filato
Shugaban kungiyar ’yan kasuwa na Jihar Filato, Mista danjuma Yerse ya rantsar da shugabannin kungiyar ’yan kasuwa na kananan hukumomin jihar guda 17 a karshen makon da ya gabata a dakin taro na Azi Nyako da ke garin Dadin-Kowa a kusa da garin Jos, babban birnin jihar.Da yake jawabi a lokacin rantsarwar, Mista danjuma ya […]
Shugaban kungiyar ’yan kasuwa na Jihar Filato, Mista danjuma Yerse ya rantsar da shugabannin kungiyar ’yan kasuwa na kananan hukumomin jihar guda 17 a karshen makon da ya gabata a dakin taro na Azi Nyako da ke garin Dadin-Kowa a kusa da garin Jos, babban birnin jihar.
Da yake jawabi a lokacin rantsarwar, Mista danjuma ya yi kira ga shugabannin su rike amanar da aka damka musu tsakani da Allah, sannan ya bukaci ’yan kasuwan jihar su hada kansu domin harkokin kasuwanci ya sami cigaba a jihar.
A nasa jawabin a madadin sauran shugabannin da aka rantsar, shugaban kungiyar na karamar Hukumar Jos ta Arewa, Alhaji dan’azumi Maigida Ibrahim ya tabbatar da cewa za su yi iyakar kokarinsu wajen kare hakki da mutuncin ’yan kasuwa dangane da harkokin kasuwancin da suke gudanarwa a jihar.
Ya yi kira ga dukkan ’yan kasuwar su cigaba da ba su hadin kai da goyan baya da shawarwari domin su cimma kudurorin da suka sanya a gaba na bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
Daga nan ya yi kira ga gwamnatin Jihar Filato ta taimaka wa ’yan kasuwa, kamar yadda wasu jihohi suke taimaka wa ’yan kasuwarsu, “Domin yin haka yana da matukar mahimmanci saboda ’yan kasuwa su ne kashin bayan tattalin arzikin kasa”. Inji shi.