An rasa rayuka a rikicin Kuros Ribas
Akalla mutum uku ne suka rasa rayukansu tare da raunaka wasu da dama a wani rikici da barke ranar Litinin a unguwannin Abanwan da Orugbam a karamar hukumar Biase ta jihar Kuros Ribas. Wani ganau kuma alkali ne daga cikin unguwannin da rikicin ya faru. Ya ce, sanadiyyar fadan fegi ne ya janyo rikicin. Yayin […]
Gwamna Ben Ayade na jihar Kuros Riba
Akalla mutum uku ne suka rasa rayukansu tare da raunaka wasu da dama a wani rikici da barke ranar Litinin a unguwannin Abanwan da Orugbam a karamar hukumar Biase ta jihar Kuros Ribas.
Wani ganau kuma alkali ne daga cikin unguwannin da rikicin ya faru. Ya ce, sanadiyyar fadan fegi ne ya janyo rikicin. Yayin da jama’ar unguwar Orugbam suka rufe hanyar zuwa unguwar Ipene tare da rushe gidajen jama’ar yankin.
A yanzu haka hukumar ‘yan sanda ta kama mutum biyar, amma daga bisani Mataimakin Gwamnan jihar ya bayar da umarnin sakinsu don tabbatar da zaman lafiya a yankin.