An rasa yara 2 da gidaje 1,100 a gobarar sansanin gudun hijira a Borno
Gobarar ta tashi a yayin da ake jimamin wadda ta yi barna a Kasuwar Gamborou a karshen mako
Kananan yara biyu sun rasu gidaje 1,113 sun kone a sakamakon gobarar da ta tashi a ranar Laraba a sansanin ’yan gudun hijira da ke yankin Muna Alamdari a Karamar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.
Gobarar ta ranar Laraba ta tashi ne a yayin da ake cikin jimamin wadda ta tashi a a karshen mako a Babbar Kasuwar Gamborou da ke Maiduguri babban birnin jihar.
Kodinetan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno a Karamar Hukumar Mafa, Surajo Garba, ya ce yara maza ’yan shekaru bakwai da 10 ne suka rasu a gobarar.
“Gidaje 1,113 sun kone, wasu 50 kuma an yi amfani da su wajen aikin agajin gaggawa,” in ji Surajo.
- An sace wayar tsohon Minista a cikin kotun Abuja
- NAJERIYA A YAU: Yadda Yajin Aiki Ya Shafi Fannin Ilimi
Ya ci gaba da cewa ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba tukuna, haka kuma ba a tantance yawan dabbobi da sauran kadarorin da gobarar ta lalata ba.
A jawabinsa bayan ziyarar gani da ido da ya kai sansanin ’yan gudun hijirar da aka samu gobarar, Darakta-Janar na hukumar, Barkindo Muhammad, ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safe, sai bayan awanni ’yan kwana-kwana da taimakon sauran hukumomi da jama’ar gari suka shawo kanta.
“Muna jajantawa kuma za mu ba da tallafin gaggawa da suka hada da buhu 500 na shinkafa, da barguna da sauran kayayyaki nan take,” in ji shi.
Ba karon farko ba ke nan a 2023
Karo na biyu ke nan da aka samu tashin gobara a sansanin, bayan makamancinsa a watan Fabrairum wanda ya kone bukkoki 200.
Wancan lokaci hukumomi sun gobarar ta tashi ne da misalin karfe 11 na safe bayan yawancin mazauna sansanin sun shiga gonaki neman abninci.
Akasarin wadanda abin ya shafa, babu abin da suka tsira da shi sai kayan jikinsu.
A watan Nuwamban 2022 an samu gobara a sansanin ’yan gudun hijirar da ke Karamar Hukumar Mafa, mako uku bayan tashin watto gobarar a sansanin ’yan gudun hijira a Karamar Hukumar Konduga da kuma wata gobarar a Maiduguri.
A watan Fabrairun 2022, wasu gidaje 100 suka kone a sansanin ’yan gudun hijira na Muna El-Badawi da ke Maiduguri a sakamakon fashewar tukunyar iskar gas.
A shekarun da suka wuce ne Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC), da kungiyoyin agaji da attajirai suka gina dubban gidaje domin sake tsugunar da ’yan gudun hijira, ko da yake har yanzu wasu dabbai na zaman jiran tsammani a matsugunan wucin gadi da aka samar musu.