An rataye masu fyaɗe 5 a Iran

Iran ta rataye wasu mutane biyar da kotu ta samu da laifin aikata fyaɗe.

An rataye masu fyaɗe 5 a Iran

Kisa ta hanyar rataya

Iran ta rataye wasu mutane biyar da kotu ta samu da laifin aikata fyaɗe.

A safiyar Laraba aka zartar da hukuncin rataya kan mutanen da kotu ta samu da laifin yi wa wata mata fyade a tare a shekarar da ta gabata.

Mutanen da aka zartar wa hukuncin ratayewa sun ɗauke matar ne da ƙarfin tuwo suka keta mutuncinta a birnin Marand da ke ƙasar, amma daga baya dubunsu ta cika.

Kwana huɗu bayan faruwar lamarin ne jami’an tsaro suka damƙe mutanen a yankin Azerbaijan da ke ƙasar kan wasu manyan laifukan na daban.

A watan Yuli Iran ta zartar da hukuncin rataya kan wasu maza huɗu da kotu ta samu da laifin aikata fyaɗe.

Kotu ta same su da laifin yi wa mata allurar kashe laka da kuma yi musu fyaɗe a wani sibitin tiyatar gyaran jiki na bogi da mutanen suka buɗe a yankin Hormozgan.