An raunata Mai Unguwa da yin garkuwa da matarsa da yara

Wasu ‘yan bindiga sun raunata Mai Unguwar Yandaka Shehu Iliyasu, da ke garin Karamar Hukumar Batsari a jihar Katsina. Bayan raunata mai unguwa da aka yi an yi garkuwa da matarsa da ‘ya’yansa uku duk a cikin gidan mai unguwar. Hukumar ‘yan sandan jihar ta tabbatarwa majiyarmu aukuwar hakan a ranar Lahadi. ‘Yan bindigan sun […]

An raunata Mai Unguwa da yin garkuwa da matarsa da yara

Wasu ‘yan bindiga sun raunata Mai Unguwar Yandaka Shehu Iliyasu, da ke garin Karamar Hukumar Batsari a jihar Katsina.

Bayan raunata mai unguwa da aka yi an yi garkuwa da matarsa da ‘ya’yansa uku duk a cikin gidan mai unguwar. Hukumar ‘yan sandan jihar ta tabbatarwa majiyarmu aukuwar hakan a ranar Lahadi.

‘Yan bindigan sun harbi Mai Unguwar akan shi da hannu, an kuma yi gaggawar kais hi asibitin Katsina daga bisani aka wuce da shi asibitin Aminu Kano don yi masa tiyata a kwakwalwa.