‘An rike sakamakon daliban FCE Zariya bayan shekaru 2 da kammala karatu’
Iyayenmu sun shiga cikin shakkun ko mun yi karatun.
Iyaye da daliban da suka kammala karatun Digiri a Kwalejin Ilimi ta Gwamnatin Tarayya (FCE) da ke Zariya, sun koka bisa rashin samun sakamakon jarabawarsu shekaru biyu da kammala karatunsu.
Sun yi wannan koke ne a lokacin da suke zantawa da manema labaru akan halin da suka sami kansu.
- Mutum 2 sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Bauchi
- ‘Yan bindiga sun sace Malamin Kwaleji a Zariya
Malam Muhammadu Sani Mudi wanda ke da ‘ya’ya biyu kuma ya yi a magana a madadin sauran iyayen daliban da ke koke, ya ce tun a watan Afirilun shekarar 2021 yaransu ke zaman jiran sakamakon jarabawarsu amma har yanzu shiru babu wani bayani.
Ya ce yaransu karatun Digiri suka yi wadda Kwalejin ke gudanarwa tare da hadin guiwa da Jami’ar Usman Dan Fodio da ke Sakkwato da kuma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
A cewarsa, wata sahihiyar majiya ta shaida cewar rashin biyan kudin da Kwalejin ta yi shi ne ya haifar da matsalar da wadannan jami’o’i suka ki sakin sakamakon jarabawar daliban.
Majiyar ta yi bayanin cewa duk da sun buya kudin makarantar da ya haura yadda daliban Jami’a ke biya amma an wayi gari Kwalejin ta kasa biyan kudaden da ya kamata ta biya domin a sami sakamakon jarabawar.
Daya daga cikin daliban da ya nemi a sakaya sunansa, ya yi bayanin cewa rashin fitar da sakamakon jarabawar ya sanya iyayensu cikin shakkun ko sun yi karatun.
Ya ce a halin da ake ciki daliban da suka kammala karatu daga wasu jami’o’i tuni suka tafi yi wa Kasa hidima amma su kuwa shiru kake ji.
Aminiya ta tuntubi Sakataren Harkokin Ilimi na Kwalejin, sai dai ya ce hurumin Jami’ar Hulda da Jama’a ta Kwalejin ce ta yi bayani a kan lamarin.
Ko da Aminiya ta ziyarci ofishinta, Hajiya Rakiya Sidi ta ce bayanin da take da shi dan kadan ne amma za ta tuntubi Shugaban Kwalejin kafin ta yi magana da mu.