An roki malaman jami’ar Gombe su kauce wa yajin aiki
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince za ta biya malaman Jami’ar Jihar hakkokinsu tare da rokonsu su janye yajin aikin da suke barazanar shiga domin kauce wa jefa daliban jami’ar cikin wani hali.Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Dokta Daniel Musa ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Gombe, […]
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince za ta biya malaman Jami’ar Jihar hakkokinsu tare da rokonsu su janye yajin aikin da suke barazanar shiga domin kauce wa jefa daliban jami’ar cikin wani hali.
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta Jihar Dokta Daniel Musa ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Gombe, bayan ganawa da Gwamnan Jihar Ibrahim dankwambo ya yi da shugabannin jami’ar a gidan gwamnatin jihar.
Ya ce gwamnatin ta amince za ta biya malaman Jami’ar Jihar duk hakkokin da suke bin gwamnati, amma bisa yanayin yadda tattalin arziki ke ciki a yanzu gwamnati ba za ta iya biyan kudin a lokaci daya ba sa dai za a rika saka musu cikin albashi daga watan farko na shekara mai zuwa. Ya ce shugabannin jami’ar, wadanda suka amince da shirin tare da fahimtar yanayin da ake ciki, sun dauki alkawarin kai sakon gwamnatin ga takwarorinsu da suka yi barazanar shiga yajin aiki da farko.
A wani taron manema labarai da malaman jami’ar jihar suka kira a kwanakin baya ne suka yi barazanar shiga yajin aikin saboda rashin biyansu hakkokinsu kamar yadda aka yi yarjejeniya da gwamnati tun a shekarar 2009, tare da zargin cewa Gwamnatin Jihar Gombe a karkashin Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ba ta bai wa jami’ar kyakkyawar kulawar da ta kamata wajen ba ta kudin gudanarwa da saka hannu wajen gine-gine da ake yi a jami’ar.
Babban Sakataren ya yi watsi da zarge-zargen tare da bayyana cewa a kowane wata ana bai wa jami’ar Naira miliyan 160, adadin da jami’ar ba ta taba samun kamarsu ba sai a wannan gwamnati.