An rufe coci saboda addabar maƙwabta da hayaniya a Oyo
An ɗauki matakin ne bayan yunƙuri da dama na sasanta masu ƙorafin da kuma hukumar cocin ya ci tura.
Gwamnatin Jihar Oyo ta rufe wata majami’a a rukunin gidaje na Golden Estate da ke unguwar Oluyole a birnin Ibadan saboda maƙwabta sun yi ƙorafi ana damunsu da ƙara a lokacin ibada a cocin.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Dotun Oyelade ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a.
- Muna buƙatar Gwamna Zulum ya rage cunkoson makabartu — Shehun Borno
- Najeriya ta kai matakin kusa da na ƙarshe a Gasar AFCON
Ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne bayan yunƙuri da dama da ma’aikatar kula da muhalli ta yi na ƙoƙarin sasanta masu ƙorafin da kuma hukumar cocin ya ci tura.
Mista Oyelade ya ce, “saboda haka ne ya kasance gwamnatin jihar ba ta da wani zaɓi da ya wuce na ta rufe cocin domin gudun kada lamarin ya ƙazanta tsakanin mazauna unguwar da cocin.”
BBC ya ruwaito cewa, a baya can mazauna unguwar sun taɓa rufe ƙofar shiga rukunin gidajen domin hana masu ibada a cocin shiga.
Gwamnatin jihar ta yi gargaɗin ɗaukar matakin shari’a a kan majami’u da masallatai da gidajen shaƙatawa da ma’aikatu da kamfanoni da kasuwanni kan buɗe lasifika ko hayaniya da za ta damu jama’a.