An rufe gidan abincin da ke sayar da naman kura a Saudiyya

An rufe wani gidan abinci a kasar Saudiyya, tare da tarar Riyal dubu 10 (Naira dubu 700) saboda sayar wa mutane naman kura.An gano gidan abinci ne mai lakabin Tekun fasha (The Gulf Restaurant) a unguwar birni da ke Surat Obaidah, bayan da aka kai wani samame. Jaridar Arabnews ta ruwaito cewa, masu bincike sun […]

An rufe gidan abincin da ke sayar da naman kura a Saudiyya
An rufe gidan abincin da ke sayar da naman kura a Saudiyya

An rufe wani gidan abinci a kasar Saudiyya, tare da tarar Riyal dubu 10 (Naira dubu 700) saboda sayar wa mutane naman kura.
An gano gidan abinci ne mai lakabin Tekun fasha (The Gulf Restaurant) a unguwar birni da ke Surat Obaidah, bayan da aka kai wani samame. Jaridar Arabnews ta ruwaito cewa, masu bincike sun gano cewa wurin girka abincin wannan gidan abinci a kulle yake kodayaushe, don haka aka kai musu farmaki har aka gano cewa naman kura suke dafawa, suna sayar wa mutane.
Hukumomi dama suna zargin gidan abincin, don haka suka killace wurin, har suka samu nasarar kwace naman kurar da suka gano ana dafawa.
Bincike ya nuna ana sayar da kilo guda na naman kurar a kan Riyal 200, wato daidai da Naira dubu 14, kodayake a wani lokaci sukan kimanta farashin naman gwargwadon yawan shekarun kurar da aka yanka.
Da jaridar Arabnews ta tuntubi wani likita kan ko naman kura na da illa ga lafiyar dan Adam, sai ya bayyana cewa, ‘binciken kimiyya bai gano wata illa da ke tattare da naman kura ba.’