An rufe gidan rediyo kan sukar juyin mulkin Nijar

Gwamnati ta rufe wani shahararren gidan rediyo a kasar Burkina Faso kan sukar juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi wa Shugaba Bazoum

An rufe gidan rediyo kan sukar juyin mulkin Nijar

Mohammed Bazoum

Gwamnati ta rufe wani shahararren gidan rediyo a kasar Burkina Faso kan sukar gwamantin sojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.

A ranar Alhamis gwamnatin sojin Burkina Faso ta rufe gidan rediyon Omega nan take, bayan wata hira da kakakin ’yan tawaye ga gwamantin sojin Nijar, Ousmane Abdoul Moumouni, da ke fafutukar dawo da Mohamed Bazoum kan mulki.

Ministan Sadarwa, Rimtalba Jean Emmanuel Ouedraogo, ya bayyana cewa kungiyar Ousmane “kira take yi karara zuwa ga tashin hankai da kuma yakar al’ummar Nijar” da nufin dawo da Bazoum “ta kowace hanya.”

A cewarsa, an rufe tashar ne domin kare muradun Burkina Faso, saboda a cewarsa, Ousmane ya ci mutuncin sabuwar gwamnatin sojin Nijar. Bayan sanarwar tashar ta daina watsa shirye-shirye.

Gwanatin sojin Burkina Faso da Mali da Guinea Bussau sun yi alkawarin taimaka wa takwarorinsu na Nijar da a halin yanzu kungiyar ta sanar da shirin far musu da karfin soji domin dawo da Shugaba Mohamed Bazoum.

Sau biyu a cikin shekara guda sojoji suka yi juyin mulki a shekarar 2022, saboda zargin gwamnatin farar hula da gazawa wajen yaki da masu ikirarin jihadi.

A bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga watan Yuli ne sojojin da takwarorinsu da suka yi juyin mulki a Mali suka bayyana goyon bayansu gare su, wajen yakar duk wanda ya kawo musu barazana.

Mali da Burkina Faso sun kori dakarun Faransa da a baya suke taimaka wa gwamnatocin kasar na farar hula yakar masu ikirarin jihadin, bisa zargin amfana da ayyukan ta’ddancin.A watanni baya sojojin Burkina Faso suka toshe shirye-shiryen tashoshin talabijin da rediyon Faransa (LCI France24 da kuma RFI) tare da korar wakilan gidajen jaridun Faransa da na Liberation da kuma Le Monde.