An rufe jaridar da ta shekara 41 a Kuwait saboda karancin jari

Ministar Kasuwanci da masana’antu na kaskar Kuwait ya kwace lasisin jaridar Al-Watan, wadda aka kafa tun a shekarar 1974, kuma mujallar masu kudin duniya ta Forbes ta bayyana cewa, shafin intanet na jaridar shi ne wanda aka fi ziyarta a daukacin Gabas ta tsakiya. Majiya ta bayyana cewa, kamafnin jaridar, wanda ya shekara 41 da […]

An rufe jaridar da ta shekara 41 a Kuwait saboda karancin jari
An rufe jaridar da ta shekara 41 a Kuwait saboda karancin jari

Ministar Kasuwanci da masana’antu na kaskar Kuwait ya kwace lasisin jaridar Al-Watan, wadda aka kafa tun a shekarar 1974, kuma mujallar masu kudin duniya ta Forbes ta bayyana cewa, shafin intanet na jaridar shi ne wanda aka fi ziyarta a daukacin Gabas ta tsakiya.

Majiya ta bayyana cewa, kamafnin jaridar, wanda ya shekara 41 da kafuwa karfin jarinsa ya yi kasa, inda ake ganin bai kai Dalar Kuwait rabin miliyan wato daidai da Naira miliyan 31
Minista Kasuwanci da Masana’antu, Abdul Mohsen Midaj ya gargadi Al Watan da sauran kamfanoni, wadanda ke fuskantar barazanar kwace lasisinsu, amtukar jarinsu ya ci gaba da yin kasa, sabanin adadin kudin da aka kayyade, kamar yadda jaridar kasar ta Al-Jareeda ta ruwaito a ranar Talatar da ta gabata.
Al-Watan na daya daga cikin manyan jaridun kasar Kuwait, kuma an kaddamar da ita ne a shekarar 1974. Sannan shafinta na intanet shi ne a biyu a jerin shafukan jaridun da aka fi ziyarta, in la’akari da binciken mujallar Forbes na shekarar 2010.
Ministan ya bayyana cewa an gargadi daruruwan kamfanoni kan rashin cika ka’idar dokar da aka kirkiro a shekarar 2012, sannnan aka yi mata gyara a shekarar 2013.
Ya ce an kulle wasu kamfanoni, wasu kuwa an gurfanar da su gaban shari’a
A wani sako da jaridar ta aike a shafin sadarwarta ta bayyana cewa ma’aikatar ta bayar da umarnin rufe jaridar. Sannan kamfanin jaridar ya bayar da sanar cewa za su daukin matain shari’a don kwatar ’yancinsu. Sannan wannan lasisi da aka kwace musu ba zai shafi kamfanin talabijin din su ba.
Tun a cikin watan Afrilun bara, an taba dakatar da buga jaridar Al-Watan har na tsawon mako biyu.
Tun cikin watan Yulin bara aka kwace lasisin Alem Al Yawm, inda hukumomi a kasar Kuwait suka bayyana cewa jaridar ta kasa cika ka’idar karbar lasisin. Don haka aka daina buga jaridar.