An rufe Kasuwar Kwanar Gafan kan tara ’yan luwadi da maɗigo

An rufe kasuwar tumatir ta Kwanar Gafan da ke Kano kan zama matattarar ’yan luwaɗi da maɗigo da ƙaruwai da sauran masu laifi.

An rufe Kasuwar Kwanar Gafan kan tara ’yan luwadi da maɗigo

Kasuwar tumatir a Katsina

Gwmanatin Jihar Kano Kano ta rufe kasuwar tumatir ta Kwanar Gafan kan ayyukan luwadi da maɗigo da kuma karuwanci.

Shugaban Ƙaramar Hukumar, Garum Malam, Barista Aminu Salisu Kadawa, ya bayyana wa Aminiya cewa, baya ga ayyukan masha’a da ake tafkwa a kasuwar, ta zamo maɓoyar ɓarayi da ’yan fashi da makami da sauransu.