An rufe Majalisar Dokokin Delta kan zaftare albashin ma’aikata

Sun nuna damuwa game da daidaita ma’aikata na yau da kullum, horar da ma’aikata .

An rufe Majalisar Dokokin Delta kan zaftare albashin ma’aikata

Ƙungiyar Ma’aikatan Majalisar Dokokin Najeriya (PASAN) ta rufe Majalisar Dokokin Jihar Delta saboda gaza cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe da Gwamna Sheriff Oborevwori ya yi dangane da sabon tsarin albashi.

Fusatattun mambobin PASAN reshen Jihar Delta, sun dakatar da duk wasu harkoki a cikin majalisar, inda suka tare kofar shiga tare da hana Shugaban Majalisar da sauran ‘yan mambobi shiga ciki.

Ma’aikatan sun nuna rashin jin daɗinsu yadda aka ɗauki tsawon lokaci ana zaftare wani kaso a albashinsu, matsalar da a yanzu an shafe shekaru uku ba tare da an warware ta ba.

Kazalika, sun nuna damuwa game da banbanci da ake nunawa a tsakanin ma’aikata, da rashin horar da ma’aikata da rashin samun wasu haƙƙoƙi daban-daban waɗanda har yanzu ba a magance su ba.

A yayin wani babban taro da aka gudanar a ranar Talata, ma’aikatan sun bayyana rashin jin daɗinsu kan abin da suka ce da gangan ake hana su haƙƙoƙinsu.

Sun ce irin wannan jinkiri ya nuna rashin kishin siyasa a ɓangaren shugabancin Majalisar da kuma gwamnati baki ɗaya.

Tags