An rufe makaranta don dalibai sun sa hijabi

An rufe makarantar sakandare mai zaman kanta ta Jami’ar Ibadan a yau Litinin bayan rikicin da ya faru sanadiyyar tasa keyar dalibai zuwa gida saboda saka Hijabi. A wata sanarwa da aka yi a kofar shiga makarantar na cewa, an rufe makarantar har zuwa wani lokaci da ba a sanar ba. Kamar yadda majiyar Kamfanin […]

An rufe makaranta don dalibai sun sa hijabi

An rufe makarantar sakandare mai zaman kanta ta Jami’ar Ibadan a yau Litinin bayan rikicin da ya faru sanadiyyar tasa keyar dalibai zuwa gida saboda saka Hijabi.

A wata sanarwa da aka yi a kofar shiga makarantar na cewa, an rufe makarantar har zuwa wani lokaci da ba a sanar ba. Kamar yadda majiyar Kamfanin Dillancin Labarai NAN ta sanar.

Iyayen daliban sun yi zargin cewa hukumar gudanarwa makarantar sakandaren ta kulle makarantar ne, tun bayan fara sanya hijabi da dalibai musulmai suka yi a makarantar.