An rufe makarantu a Adamawa

Gwamnatin Jihar Adamawa ta rufe daukacin makaratun da ke jihar a dukkanin matakai nan domin takaita yaduwar cutar COVID-19. Ta bayar da umarnin bayan Gwamantin Tarayya ta umarci a ci gaba da kiyaye matakan kariyar COVID-19 wadda ta ke kara bazuwa a karo na biyu a Najerya. Daliban Kankara sun sauka a Gidan Gwamnatin Katsina […]

An rufe makarantu a Adamawa

Daya daga cikin azuzuwan makarantun

Gwamnatin Jihar Adamawa ta rufe daukacin makaratun da ke jihar a dukkanin matakai nan domin takaita yaduwar cutar COVID-19.

Ta bayar da umarnin bayan Gwamantin Tarayya ta umarci a ci gaba da kiyaye matakan kariyar COVID-19 wadda ta ke kara bazuwa a karo na biyu a Najerya.

Babbar Sakatare a Ma’aikatar Ilimi da Inganta Rayuwa, Aishatu Abubakar ta ce: “Ma’aikatar na umartar a rufe dukkannin makarantu nan take daga ranar 17 ga Disamba, 2020.

“Za a sanar da ranar budewa nan gaba, saboda haka shugabannin dukkanin makarantu su kiyaye.”

Sanarwar na zuwa ne kwana guda bayan jihar Kaduna ta dauki makancin matakin bayan yaduwar cutar a jihar.

Jihar Kano ma ta rufe dukkannin makarantu duk da cewa ba ta bayyana dalilin daukar matakin ba.

Sai dai jihar na daga cikin wadanda a baya-bayan nan suka nuna damuwarsu game da karuwar masu kamuwa da cutar ta COVID-19.