An rufe makarantu masu zaman kansu 300 a Neja

Fiye da makarantu masu zaman kansu 300 da suka saba wa ka’idoji ne Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja ta rufe a sassan jihar a daya daga cikin matakan da gwamnati ke dauka don farfado da ilimi da ba shi kular da ta kamata.Kwamishinan Ilimi na Jihar, Malam danladi Umar Abdul-Hameed ne ya fadi haka, yayin […]

An rufe makarantu masu zaman kansu 300 a Neja

Fiye da makarantu masu zaman kansu 300 da suka saba wa ka’idoji ne Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Neja ta rufe a sassan jihar a daya daga cikin matakan da gwamnati ke dauka don farfado da ilimi da ba shi kular da ta kamata.
Kwamishinan Ilimi na Jihar, Malam danladi Umar Abdul-Hameed ne ya fadi haka, yayin da suke ganawa da wakilinmu a ofishinsa, inda ya ce daga cikin ka’idojin da masu makarantun suka kasa cikawa akwai rashin samar da isassun ajujuwan daukar darussa da rashin filayen wasa don walwalar dalibai.
Malam danladi Umar ya ce, wasu daga cikin masu maka-rantun sun kama gidajen haya ne suke gudanar da harkokinsu, tare da keta sharudda da dama.
Kwamishinan ya ce ma’aikatar tana gudanar da bincike game da zargin da ake yi wa wasu daga cikin jami’an ma’aikatar da ke amsar na goro don saba wa sharuddan da aka gindaya ga masu bukatar bude makarantu masu zaman kansu, domin hukunta su.
Ya yi kira ga iyaye su rika bincikar makarantun da suke sha’awar tura ’ya’yansu domin neman ilimi, ya ce gwamnatin jihar ta samar da yanayin da ya kamata don koyarwa, kuma makarantun gwamnati na iya goga kafada da masu zaman kansu.
Game da cunkoson dalibai da karancin malamai a makarantun gwamnati, ya ce gwamnati tana kara yawan ajujuwa a makarantun karkara da birane.Wannan ya sa a bana aka bude wasu sababbin makarantu a sassan jihar.Ya kara da cewa malaman da ke koyarwa suna da takardar shaidar malanta ta kasa.