An rufe makarantu saboda cutar kyanda a Adamawa

An rufe makarantun kudi da na gwamnati bayan cutar kyanda ta yi ajalin kananan yara dama da 42ba Jihar Adamawa

An rufe makarantu saboda cutar kyanda a Adamawa

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri

Gwamnatin Adamawa ta rufe daukacin makarantu da ke jihar sakamakon annobar cutar kyanda.

Sanarwar rufe makarantun da aka fitar ranar Litinin ta ce umarnin ya shafi makarantu masu zaman kansu da na gwamnati da ke fadin jihar.

Ma’aikatar ilimi ta jihar ta ce an rufe makarantun ne domin ba awa hukumar lafiya a matakin farko ta jihar damar yi wa kananan yara allurar riga-kafin cutar.

Kawo yanzu cutar kyanda ta yi ajalin kananan yara akalla 42 a jihar.

Hukumar ta ce ana sa ran nan gaba za a bude makarantun a ranar 13 ga watan nan na Mayu.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania