An rufe makarantun Firamare dubu a Pakistan

Hukumomin Lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke kasar Pakistan sun kulle makarantun Firamare dubu saboda karancin masu shiga, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito. Sun ce gine-ginen mkarantun da aka yi watsi da su, an kashe biliyoyin kudi wajen gina su, inda sashen ilimi ya kai su wuraren da ba su dace ba, ta wajen […]

An rufe makarantun Firamare dubu a Pakistan
An rufe makarantun Firamare dubu a Pakistan

Hukumomin Lardin Khyber Pakhtunkhwa da ke kasar Pakistan sun kulle makarantun Firamare dubu saboda karancin masu shiga, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.

Sun ce gine-ginen mkarantun da aka yi watsi da su, an kashe biliyoyin kudi wajen gina su, inda sashen ilimi ya kai su wuraren da ba su dace ba, ta wajen saba wa ka’idar umarnin da aka bayar kan yadda masu mulki za su tursasa wadanda suka kada musu kuri’u.

Wani babban jami’in hukuma ya bayyana wa kafar labarai ta Dawn a Litinin din da ta gabata cewa sashen ilimi ba ya da katabus kan al’amarin, domin sun bi umarnin Babban minista Perbez Khattak.

“Ba mu da karfin ikon yanke matsaya kan wurin da za a gina makaranta, sabanin haka ma umarni muke karba daga babban minista Perbez Khattak.

Jami’in ya cera’ayin sashen ilimi watsi ake yi da shi a wajen gina sababbbin makarantu, sabanin haka ma, makarantun ana gina su ne duk inda babban minista ke bukata.

Jami’in ilimi wata gunduma cewa ya yi, sashen ilimi ya rufe makarantun ne saboda karancin daliban da ke dauka, wadanda suke kkasa da 40, kamar yadda kafar labarai ta Dawn news ta ruwaito.

Ya ce mafi yawan makarantun da aka rufe an gina su ne a yankunan karkara.

Bisa kimar da gwamnati ta fitar, za a gina sabuwar makaranta ne a al’ummar da yawanta ya kai dubu, inda ake da tabbacin samun daliban da za su shiga makaranta 160.