An rufe Masallacin Juma’a kan rikicin limanci a Legas
An ba hamata iska a yayin da ake shirin Sallar Juma’a tsakanin wasu malamai da ke rikicin limanci a Babban Masallacin Epe
An ba hamata iska a yayin da ake shirin Sallar Juma’a, a tsakanin magoya bayan wasu malamai da ke rikicin limanci a Babban Masallacin Epe da ke yankin Ita Opo a Jihar Legas.
A kan hakan ne Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda mai kula Shiyya ta biyu, ya ba da umarnin rufe masallacin har sai an sasanta rikicin.
- Gobara ta tashi a Kotun Kolin Najeriya
- A wata 4 Tinubu ya ciwo bashin tiriliyan 1.6 daga Bankin Duniya
Wasu malamai biyu marasa ga maciji da juna ne dai ke rikicin, inda kowannensu ke ikirarin zama Babban Limamin masallacin.
A ranar Juma’a ne lamarin ya yi tsanani, inda kowanne daga cikinsu ya yi kokarin jagoranar Sallar Juma’a, wanda a sanadin haka rikici ya barke.
Wani bidiyon da aka sanya a kafofin sada zumunta ya nuna ’yan sanda sun yi awon gaba da Babban Limamin Masallacin, Alhaji Abdullateef Oladapo.
Daga baya wasu malamai biyu, ciki har da Alhaji Abdulkabir Oriyomi suka yi ta kokarin jagorantar Sallar Juma’ar.
Aminiya ta gano cewa, ganin cewa akwai yiwuwar samun rikici ne ya ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar,Obafemi Hamzat, ya girke ’yan sanda domin tabbatar da doka da oda a masallacin.
Amma duk da haka kowanne daga cikin malaman ke neman sai ya jagoranci Sallar Juma’a, wanda hakan ta sa aka tsare Oladapo, lamarin da bai wa magoa bayansa dadi ba.
Daga bisani dattawan yankin suka sa baki aka sako bisa inda ya dauki alkawarin ba za a sake samun sa da hannu a rikici ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa al’ummar yankin sun cire Oladapo daga limanci ne saboda zargin sa da fadin rai da kuma zafafawa, zargin da ya musa.
Daga nan aka mayar da shi Babban Limamin unguwar Oriyomi da ke yankin na Epe.
Wani dan kwamitin zaman lafiyar masallacin, Alhaji Fariu Arebi ya shaida wa wakilinmu cewa suna kokarin sasanta matsalar da kuma ganin an sake bude masallacin.
Wani mazaunin yankin ya saida wa wakilin namu cewa rikicin limancin yana dadadden tarihi tsakanin ’yan kabilar Epe-Lagos da kuma Epe-Ijebu ya salin Jihar Ogun.