An rufe sakatariyar dukkan Kananan Hukumomin Filato
Rikicin shugabanci na ci gaba da kamari a jihar.
Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin rufe ilahirin sakatariyar Kananan Hukumomin Jihar Filato 17, biyo bayan rikicin da ya barke a jihar.
Aminiya ta rawaito cewa Gwamna Caleb Mutfuwang da aka rantsar mako biyu da suka gabata ya dakatar da Ciyamomin jihar su 17 ne bisa zargin karkatar da kudade.
- Chukkol ya maye gurbin Bawa a matsayin Shugaban EFCC na rikon kwarya
- Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi
Ya nada shugabannin rikon kwarya da za su rika kula da Kananan Hukumomin, amma dakatattun shugabannin sun bijire tare da bayyana cewa Gwamna ba shi da hurumin dakatar da su.
Sun ci gaba da aiki a matsayin Shugabannin Kananan Hukumominsu, lamarin da ya kusan kai ga rushewar doka da oda a ranar Laraba.
Amma a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Alabo Alfred, ya ce Sufeton ya umarci Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Bartholomew Onyeka, da ya rufe dukkan hedkwatocin 17.
“Daukar matakin ya zama dole sakamakon tashe-tashen hankula a tsakanin Shugabannin Kananan Hukumomin, da kuma barazanar da magoya bayansu ke yi ga muhimman ababen more rayuwa, rayuka da dukiyoyi a jihar.
“Shawarar daukar wannan mataki ya yi daidai da aikin da kundin tsarin mulkin kasa ya ba mu a matsayinmu na rundunar ’yan sandan Najeriya, don tabbatar da cewa abun bai yi tasiri a Filato ba.
“Don haka, rundunar ’yan sandan Najeriya a Filato ba za ta zauna ta kalli yadda al’amura ke tafiya ba daidai ba a karkashin kulawarmu, don haka akwai bukatar daukar wannan muhimmin mataki na rufe sakatarorin kananan hukumomi.
“Saboda haka rundunar ta yi gargadin cewa ba za ta yi wasa da duk wanda ya yi kokarin kawo cikas ko kawo rudani a cikin sakatarorin kananan hukumomin ba, domin za mu tabbatar da cewa doka ta yi aiki a kan wadannan mutane.”
A ranar Talata ce wasu mazauna jihar suka gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga rikicin shugabancin da ya ki ci ya ki cinyewa a Kananan Hukumomin Jihar.