An rufe shafukan sada zumunta don jarabawa a Habasha

Hukumomi a kasar Habasha sun rufe shafukan sada zumunta da muhawara a lokacin da dalibai ke gudanar da jarabawar shiga jami’a.Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato wani kakakin gwamnatin kasar na cewa an rufe shafukan ne domin “kada su dauke hankulan daliban masu daukar jarabawa.”An yi satar amsar wasu darussa inda aka wallafa su a […]

An rufe shafukan sada zumunta don jarabawa a Habasha
An rufe shafukan sada zumunta don jarabawa a Habasha

Hukumomi a kasar Habasha sun rufe shafukan sada zumunta da muhawara a lokacin da dalibai ke gudanar da jarabawar shiga jami’a.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ambato wani kakakin gwamnatin kasar na cewa an rufe shafukan ne domin “kada su dauke hankulan daliban masu daukar jarabawa.”
An yi satar amsar wasu darussa inda aka wallafa su a shafukan intanet a watan jiya, lamarin da ya sa aka soke yin jarabawarsu a lokacin.
AFP ya ce ba a iya shiga shafukan Facebook, Twitter, Instagram da kuma biber tun daga ranar Asabar din da ta wuce.
Kakakin gwamnatin, Getachew Reda ya ce, “an rufe shafukan sada zumunta kuma sai ranar Laraba za a bude. Shafukan suna dauke hankulan dalibai.”
Sai dai wani fitaccen mai fafutika a shafukan sada zumunta Daniel Berhane ya yi tur da wannan mataki.
Gwamnatin kasar Habasha tana sanya ido sosai kan kafofin yada labaran kasar, inda galibin jama’a suke dogara da shafukan sada zumunta don samun labarai musamman wadanda ba za su iya wa gwamnatin dadi ba.
Har ila yau, a makon jiya ne Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar dinkin Duniya, inda ta ce sanya ido da gwamnatin take a kafofin yada labarai keta hakkin dan Adam ne.