An rufe ta a daki shekara biyu saboda tana son komawa wajen tsohon mijinta

A ranar Litinin da gabata ce aka gano wata mata da ’yan uwanta suka rufe ta a cikin daki kusan shekara biyu saboda tana son komawa wajen tsohon mijinta a Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna. Matar mai suna Hassana Saleh ana zargin wai wanta mai suna Lawal Saleh ne ya rufe ta […]

An rufe ta a daki shekara biyu saboda tana son komawa wajen tsohon mijinta

Hassanah Saleh ke nan a cikin xakin da aka kulle ta

A ranar Litinin da gabata ce aka gano wata mata da ’yan uwanta suka rufe ta a cikin daki kusan shekara biyu saboda tana son komawa wajen tsohon mijinta a Rigasa da ke Karamar Hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Matar mai suna Hassana Saleh ana zargin wai wanta mai suna Lawal Saleh ne ya rufe ta a daki na tsawon wannan shekaru a dakin, inda aka ce take fitsari da bayan gida da cin abinci duk a ciki.

Wakilinmu ya samu labarin cewa sai da ’yan sanda suka yi amfani da wani karfe wajen balle kwadon da aka yi amfani da shi wajen rufe dakin da take ciki wanda kuma ke da duhu.

Wata Gidauniya mai Suna Arrida ce suka gano Hassana a inda aka kulle ta bayan samun labarin halin da take ciki a tsawon wannan shekara biyu.

Shugaban Gidauniyar Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wacce tana cikin wadanda suka ceto Hassana ta ce wai wan Hassana, Lawal Saleh ya ce sun rufeta a dakin ne saboda nacewa da ta yi sai ta koma gidan mijinta.

Ya kara da cewa a ganinsu mijinta ba ya kaunarta wanda hakan ya sa ya saketa wanda a cewarsu sakin ne ya jefata cikin damuwa.

“sun dauki matakin rufeta ne a cikin wannan daki saboda a ganinsu hakan ya zama musu dole. Ta ce za a kai matar asibiti domin a duba lafiyarsa. Muna kuma yin kiran da masu hannu da shuni da su kawo mata dauki domin tana bukatar taimako,” inji shugabar gidauniyar.

Da yake jawabi ga manema labarai a hedkawatar ’yan sandan Jihar Kaduna, wan Hassana Lawal Saleh ya ce ya rasa abin yi ne saboda Hassana tana gudu shi ya sa ya dauki wannan mataki.

“ba na gari, da na dawo gida ne aka sanar da ni cewa mijinta ya saketa kuma wai ta gudu. A lokacin da aka same ta sai kawota gidana inda nake zaune da matana hudu da ’ya’ya 41 a Rigasa.  Na yi duk mai yiwuwa domin nema mata magani amma a kullum so take ta gudu ta koma wajen tsohon mijinta.

“Daga baya sai ta sake aure inda ta aure wani mutum amma sai ta ki zama a gidan sabon mijinta saboda tana son komawa gidan tsohon mijinta kuma mahaifin ’ya’yanta,” inji shi.

Ya kara da cewa ya yanke shawarar kulle ta ne a dakin saboda ba zai iya ci gaba da daukar nauyin magungunanta ba domin abinci ma ya gagareshi a gidansa.

A kan zargin ya rufe kanwarsa shekara biyu a daki ba bisa ka’ida ba sai ya ce, sai ya ce, “wata bakwai ne kawai ta yi ba shekara biyu ba.” Game da yanayin dakin da take ciki sai ya kara da cewa ’yan uwanta mata biyu na zuwa suna mata wanka sannan kuma su share mata daki a wasu lokutan.

“Duk makwabtanmu suna sane da labarinta kuma su ne suke dawo da ita gida a duk lokacin da ta gudu. Ina mata fatan Allah Ya ba ta lafiya domin ta samu rayuwa ingantattciya.”