An rusa Kasuwar Barci da ke Kaduna
An fara rusa Kasuwar Barci da ke Tudun Wadan Kaduna a yau. Aminiya ta samu bayanin cewa, an fara rusa kasuwar ne da tsakiyar daren ranar Talata. Lokacin da jami’an Hukumar Kula da Tsare-tsaren Birnin Kaduna (KASUPDA) suka yi dirar mikiya tare da jami’an tsaro. Bayan sun rusa kamar shaguna10 sai suka yi tafiyarsu ganin […]
Shagunan kasuwar Barci
An fara rusa Kasuwar Barci da ke Tudun Wadan Kaduna a yau.
Aminiya ta samu bayanin cewa, an fara rusa kasuwar ne da tsakiyar daren ranar Talata.
Lokacin da jami’an Hukumar Kula da Tsare-tsaren Birnin Kaduna (KASUPDA) suka yi dirar mikiya tare da jami’an tsaro.
Bayan sun rusa kamar shaguna10 sai suka yi tafiyarsu ganin hakan ne yasa ’yan kasuwar tare da matasa suka fara rusa shagunansu tare kuma cire karafa da tagogi da sauran duk wani abu mai amfani.
Samari kuma na ta ci gaba da kwashe katakai da sauran ababe da aka cire a gina-ginen da aka rusa.
Wakilinmu wanda ya ziyarci kasuwar da yammacin yau ya ruwaito cewa, hankalin ’yan kasuwar duk a tashe yake yadda suke kallon ana rusa shagunansu.
Duk kokarin da ‘yan kasuwan suka yi domin neman Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai ya daga masu kafa, ya ci tura wanda hakan yasa dole suka mika lamarinsu ga Allah.