An sa dokar hana zirga-zirga tsawon sa’a 24 a Jos

Dokar ta fara aiki ne daga karfe 12 na dare a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024.

An sa dokar hana zirga-zirga tsawon sa’a 24 a Jos

Yankin da ak fi samun cunkoson ababen hawa a kasuwar ‘Yan Kura da ke Sabon Gari a Kano a lokacin dokar kulle

Gwamnati ta sa dokar hana zirga-zirga ta tsawon sa’a 24 a Karamar Hukumar Jos ta Arewa da ke Jihar Filato.

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce an sa wannan dokar hana zirga-zirga ne da nufin dakile ayyukan bata-gari da suka fake da zanga-zangar tsadar rayuwa suka kaddamar da hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Gwamnan ya sanar ce dokar hana fitar ta fara aiki ne daga karfe 12 na dare a ranar Lahadi, 4 ga watan Agusta, 2024.

Sanarwar da daraktan yada labaransa, Gyang Bere, ya fitar a daren ta ce an sa dokar ne bayan bata-gari dauke makamai sun fasa shaguna da gidajen abinci suka wawashe kayayyaki a kan hanyar Bauchi da mahadar Zololo a karamar hukumar.

“Wannan dokar hana zirga-zirga ita ce mafi amfani ga al’umma don haka ya kamata kowa ya bi ta domin tabbatar da tsaro da walwalar daukacin mazauna yankin.

“Gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su tabbatar da aiwatar da dokar hana zirga-zirgar a fadin karamar hukumar.

“Ya kuma gargadi masu shirin kara kai wa jama’a ko kayan al’umma hari da su gaggauta sauya  tunaninsu ko kuma su fuskanci fushin doka.

“Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su kasance masu taka-tsan-tsan da kuma zage damtse wajen gudanar da ayyukansu domin dakile duk wani abu da zai iya kawo cikas ga doka da oda.

“Kazalika ya nuna godiya ga al’ummar jihar musamman malaman addini bisa goyon bayan da suke bai wa manufofi da shirye-shiryen gwamnatinsa.

“Ya jinjina wa hadin kai da bin umarninsu a yayin zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar, ya kuma yaba da kudurinsu na wanzar da zaman lafiya da hadin kai,” in ji sanarwar.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki