An sa mata zaga gari da mijinta a kafada bayan kama ta da kwarto

Jama’ar gari sun tilasta wata matar aure daukar majinta a kafada ta zaga da shi a unguwa bayan an kama ta da laifin cin amanar aure.

An sa mata zaga gari da mijinta a kafada bayan kama ta da kwarto

Jama’ar gari sun tilasta wata matar aure daukar majinta a kafada ta zaga da shi a unguwa bayan an kama ta da laifin cin amanar aure.

Wannan abin ya faru ne a kauyen Borpadaw da ke kasar Indiya a farkon wannan wata da ake ciki.

Bayanai daga yankin sun nuna matar da lamarin ya shafa ta yi batar dabo na tsawon mako guda,  lamarin da ya sa mijinta da surukanta bazama neman ta amma suka rasa.

Daga nan ne mijin ya kai rahoton bacewar matar tasa ga hukuma inda daga bisani wani ya kwarmata wa hukumar cewa matar na nan a gidan saurayinta.

Bayan an gano ta a gidan kwarton ne mijin ya fusata ainun wanda hakan ya sa ya lakada mata duka da kuma jan ta a kasa.

Bayan haka ne sai mutanen gari suka tilasta matar ta dauki maigidanta a kafada ta yawata da shi a cikin unguwa a matsayin horo kan abin da ta aikata.

An ga hoton yadda mutanen suka ciccibi magidancin suka dora shi ya zauna a kafadar matar.

Haka dai ta saba mijin nata a kafada ta yi yawo da shi yayin da jama’ar gari ke biye da ita.

Da alama dai wannan mataki bai yi wa hukumar yankin dadi ba, domin tuni aka damke wasu mutum tara da ake zargi suna da hannu cikin hukuncin, yayin da ita matar kuma an tura ta gidan iyayenta.