An sa ranar nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau
Gwamna El-Rufai zai kasance babban bako na musamman a yayin bikin nadin.
Wani rahoto da BBC ya wallafa ya ce za a yi nadin sarautar sabon Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a ranar Litinin 9 ga watan Nuwamban 2020.
Rahoton ya ce wata sanarwar da aka fitar a ranar Litinin ce ta fayyace hakan mai dauke da sa hannun Shugaban Kwamitin shirye-shirye nadin, Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Muhammad Aminu.
- An sake kama Naziru Sarkin Waka
- Za a yi wa ‘yan sandan da aka kashe a zanga-zangar #EndSARS karin girma
Ana sa ran Gwamna Mallam Nasir Ahmed El-Rufai zai kasance Babban Bako na Musamman a wurin bikin nadin sarautar.
Sauran manyan baki da za su halarci taron wanda za a gudanar a filin Polo da ke Unguwar GRA a garin Zariya, sun kunshi manyan jami’an Gwamnati, ’Yan kasuwa, ’yan siyasa da sauransu.
Ambasada Bamalli ya zama sarki na farko daga gidan Sarautar Mallawa tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Alu Dan Sidi, shekara 100 da suka gabata.
Nadinsa a matsayin Sarkin Zazzau na 19 ya biyo bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris, Sarki na 18 wanda ya mutu a ranar Lahadi, 20 ga Satumbar 2020 bayan ya yi shekaru 45 yana mulki.
Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau, rawanin da mahaifinsa marigayi Nuhu Bamalli ya daura yayin da kakansa, Dan Sidi, shi ne sarkin Zazzau na 13, wanda ya yi sarauta tsakanin 1903 da 1920.
Sai dai har ila yau, Babbar Kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya, tana ci gaba da sauraron shari’ar da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar, yana kalubalantar nadin da aka yi wa Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.
Alhaji Bashar Aminu ya garzaya kotun domin neman ta ayyana shi a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19 tare da soke nadin Sarki Ahmed Nuhu Bamalli domin a cewarsa an yi nadin ta hanyar da ba dace ba.