An sa tsuntsun da ya kashe mai shi a kasuwa
Mako biyu da suka wuce mun ruwaito cewa, wani babban tsuntsu da ake kira Cassowary da yake da dogayen faratu a kafafunsa ya kashe mutumin da ya mallake shi mai suna Marbin Hojas a gidan da ake kiwonsa a garin Gainesbille a Lardin Alachua da ke Jihar Florida a Amurka. A cewar Ma’aikatan gidan Zoo […]
Mako biyu da suka wuce mun ruwaito cewa, wani babban tsuntsu da ake kira Cassowary da yake da dogayen faratu a kafafunsa ya kashe mutumin da ya mallake shi mai suna Marbin Hojas a gidan da ake kiwonsa a garin Gainesbille a Lardin Alachua da ke Jihar Florida a Amurka.
A cewar Ma’aikatan gidan Zoo na San Diego, Cassowary na daya daga cikin tsuntsaye mafiya hadari a duniya. An sanya tsuntsun na Cassowary da sauran dabbobin Marbin Hojas a kasuwar baja kolin dabbobi ta ‘Gulf Coast Libestock Auction’ a ranar Asabar da gabata.
Kasuwar baje kolin dabbobin ta Gulf Coast Libestock Auction ta wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook cewa, “Daya daga cikin burin Marbin, shi ne a sanya dabbobinsa a kasuwar baje-koli.” Rukunin masu kasuwar baje-kolin sun ce, sun yi babban rashi na Marbin Hojas.
Rahoton ya kara da cewa, ba kawai Cassowary za a sa kasuwa ba, har da sauran dabbobin Marbin Hojas. Tsuntsun Cassowary yana da girma kuna ba ya tashi sama, amma kuma yana iya tsallen mita 7, kuma zai iya gudun mil 31 a awa daya, sannan zai iya yin nikaya yayin da zai kare kansa daga barazanar sauran dabbobi.