An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari

Rarara ya ce watanni uku na farkon mulkin Tinubu, sun fi shekara 8 na Buhari

An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari

Rarara da Buhari

Bisa ga dukkan alamu, an sa zare tsakanin fitaccen mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara da magoya bayan tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Lamarin ya fara ne bayan wani taron manema labarai da mawakin, wanda ya shahara wajen wake Buhari da tallata manufofinsa a zamanin mulkinsa, ya kira a Kano da yammacin Alhamis.

A yayin taron dai, Rarara ya zargi tsohon shugaban da lalata kowanne fanni na Najeriya kafin ya mika ta ga magajinsa, wato Shugaba Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu da ya gabata.

Mawakin ya kuma nuna nadamarsa ta goyon bayan Buharin a baya, inda ya ce ya yi da-na-sanin yin hakan.

A cewarsa, “Na yi nadamar goyon bayan Buhari, saboda na yi zaton zai gyara Najeriya, amma hakan ba ta samu ba. Buhari ya gurgunta dukkan hukumomin gwamnati, dole sai an farfado da su.”

Ya kuma ce hatta watanni uku na farkon mulki Tinubu, sun fi shekaru takwas na mulkin Buhari.

Mawakin ya kuma ce hatta a kan batun nadin ministoci a gwamnatin, kamata ya yi a ce an nemi shawararsa kafin a nada su.

Rarara ya ce akalla idan ma ba a ba shi kujerar Minista ba, to kamata ya yi a ce an yi kasafinsu da shi.

Ya kuma yi zargin cewa an nada makiyan Tinubu da dama mukamai a cikin kunshin gwamnatinsa.

Rarara ya kuma bigi kirjin cewa a duk fadin Arewacin Najeriya, idan ban da tsohon Gwamnan Kano, Abdulahi Umar Ganduje da na Katsina, Aminu Bello Masari, babu wanda ya ba tafiyar Tinubu gudunmawa kamar shi.

Sai dai ya ce babu wasu kudade da ya amfana da su a gwamnatin Buhari, inda ya kalubalanci masu ikirarin da su kawo hujjar hakan.

To sai dai bullar kalaman ke da wuya, wasu Hadiman tsohon Shugaban, irin su mai taimaka masa kan harkokin kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, suka shiga yi masa lugude.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook da yammacin Alhamis, Bashir ya kwatanta kalaman na Rarara da butulci ga tsohon ubangidan nasa, inda ya ce duk wata daukaka da mawakin ya samu, sanadiyyar alakanta kansa da Buhari ce.

Ya ce “Na kalli wani bangare na videon da yake yawo na taron manema labarai da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya gabatar a yau, musamman bangarorin da ya ci wa tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari mutunci tare da zargin cewa sai da ya rusa kasar baki daya kafin ya bar mulki.

“Bayan kammala kallon video na yi yunkurin bawa Rarara amsa daya bayan daya ga duk wadannan zarge – zargen da yayi, sai dai daga bisani da na sake yin nazari a tsanake sai na ga babu bukatar hakan a halkance da kuma mutunce, saboda wasu dalilai kwarara guda biyu.

“Na farko, cikin videon, Rarara yayi ikirarin cewa wai gudunmawar daya bayar a tafiyar Buhari ko shi Buharin bai bawa kan sa irin wannnan gudunmawa ba. IKON ALLAH. Don Allah akwai hankali a cikin wannan magana?

“Sai dalili na biyu, inda yake cewa a wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu idan har ba a bashi mukamin minista ba, to ya kamata a ce an kira shi an zauna da shi an zabi wadanda za a bawa mukaman na ministoci. TASHIN HANKALI. Ko akwai chemistry, balle technology a cikin wannan batu?

“To gaskiya wanda maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a bashi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne, domin kuwa wadannan maganganun na sa sun saba da kowane irin hankali da tunani, idan dai ba akwai rashin lafiya ba, to lalle akwai tsantsar jahilci. Babu hikima a cikin maganganun nasa ko kadan.

“Game da wakokin da yayi wa Baba Buhari, tunda Rarara yake yi masa waka, bai taba yi masa waka kyauta ba tare da an biya shi hakkin sa ba,” kamar yadda Bashir ya wallafa.

HOTUNA: Yadda Rarara ya raba motoci da wayoyi a gasar wakar Tinubu

Tuni dai mutane da dama suka shiga tofa albarkacin bakinsu kan lamarin, musamman a kafafen sada zumunta na zamani.

A cewar dan jarida kuma mawallafin jaridar intanet ta Daily Nigerian, Jaafar Jaafar cewz ya yi “Matsalar Rarara ita ce: bai sani ba, kuma bai san bai sani ba.

“Duk shaharar da Shata ya yi a fagen waka da kima da yake da ita a idon manya, ba ya nuna shi wani ne kamar yadda Wawawa ke yi,” in ji Jaafar.

Shi kuwa wani mai amfani da shafin sada zumunta na Facebook cewa ya yi, “Duk butulcin da Rarara yayiwa buhari fa to bai Kai butulcin da buhari yayiwa Yan Nigeria ba”

 

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC