An sa zare tsakanin ’yan fim da ’yan downloading
An dauki tsawon lokaci ana dauki ba dadi tsakanin kungiyar da ke kare hakkin masu fina-finai tare da yaki da masu yi musu satar fasaha ta kowace irin hanya da kuma kungiyar Masu Downloading ta Jihar Kano wato kungiyar da ke daukar fina-finai da wakoki suna turawa a cikin waya a kan abin da ya […]
An dauki tsawon lokaci ana dauki ba dadi tsakanin kungiyar da ke kare hakkin masu fina-finai tare da yaki da masu yi musu satar fasaha ta kowace irin hanya da kuma kungiyar Masu Downloading ta Jihar Kano wato kungiyar da ke daukar fina-finai da wakoki suna turawa a cikin waya a kan abin da ya shafi gudanar da sana’arsu.
Sai dai a yanzu abin ya zafafa kasancewar dukkan bangarorin biyu suna zargin juna da cin zarafi da kuma take hakki.
Shugaban kungiyar Kare Hakkin Masu Fim din Hausa, reshen Jihar Kano, Alhaji Nura Magaji ya ce ba za su zura ido suna kallon masu downloading suna ci da guminsu ba.
Ya ce: “Mun dade muna jan kunnen wadannan mutane masu yi mana satar fasaha, amma ba sa ji sai da ta kai mu muna bin shagunansu muna kama su tare da gurfanar da su gaban shari’a. A kwanakin baya abin ya baci ta yadda sai da ta kai mun zura wa lamarin ido. Amma a yanzu mun sake waiwayar su saboda harkar tasu tana cutar da mu. Abin takaici ne a ce mutum ya zuba jarinsa ya yi fim, amma ba za a saya ba, saboda mutane suna zuwa suna samun sa a farashi mai rahusa wanda bai wuce Naira 20 zuwa 50 ba. Ba zai yiwu mu zuba ido mu bar abubuwa su rika tafiya haka ba, dole ne mu dauki matakin da ya dace a kan wannan lamari.” Inji shi.
Ya ce, a yanzu haka kungiyarsu na gudanar da zagaye na musamman ba wai kawai a kasuwannin Jihar Kano da shagunan masu downloading ba har da cikin wasu jihohi don kokarin dakile harkokin masu satar fasaha a sanarsu ta fim din Hausa.
Shugaban ya zargi Hukumar Kare Hakkin Mallaka ta kasa (Copy Right Commission) da kin daukar matakin da ya dace a kan wadanan mutane.
“Akwai lokutan da muka je har Abuja don gabatar da kokenmu game da satar fasaha da ake yi mana, ba wai kawai masu downloading ba, akwai mutanen da suke yi mana satar fasaha ta hanyar daukar fina-finanmu, suna sanya wa a faya-fayan CD suna sayarwa a kan farashi mai rahusa.
“Akwai mutumin da muka taba kamawa a Kano, yana sayar da wani fim din Hausa Naira 50, bayan shi mai fim din yana sayar da shi a kan Naira 180. Da muka kai wannan lamari gaban wannan hukuma har zuwa yanzu ba a yi masa wani hukunci ba. Ka ga wannan abu ne da bai dace ba.” Inji shi.
Sai dai a nasu bangaren kungiyar masu downloading din ta bakin Shugabanta Sulaiman Umar ya ce ’yan kungiyarsu na kokawa game da cin zarafin da masu sana’ar shirya fim ke yi musu ta yadda suke kama su tare da gurfanar da su gaban kotu ba tare da samunsu da laifi ba.
“A da kafin abubuwan su baci idan an shiga shagon ‘yan kungiyarmu, an samu kwamfuta a kan dauke su zuwa ofishin ’yan sanda, daga bisani a gurfanar da su gaban kotu. Amma yanzu da zarar an kama mutanenmu sai a dauke su kai tsaye zuwa kotu. Idan har ba mu samu labari a kan lokaci mun bi kadin zancen ba, sai ka ga har an kai ga cin tarar su ba tare da cikakken bincike ba.” Inji shi.
Shugaba Sulaiman ya shaida wa Aminiya cewa tun farko suna gudanar da sana’arsu ne ta hanyar daukar wakokin yabon Annabi da karatuttuka, inda suke turawa a wayoyin mutane ana ba su Naira 50, daga baya ne kuma suka tsunduma harkar fina-finan Hausa.
A cewarsa kungiyarsu a shirye take ta tattauna da kungiyar kare hakkin masu fina-finai ta jihar don yin sulhu a tsakaninsu.
“Duba da cewa muna amfana da ayyukan wadannan mutane (‘yan fim), muna neman mu zauna a teburin sulhu tare da su don tattaunawa a kan yadda za mu bullowa lamarin, idan ta kama za mu rika biyan su wani abu ne daga abin da muke karba idan mun yi amfani da ayyukansu, to wannan babu laifi. “ Inji shi.