An sabunta dokokin tsaron garejin Akinyele

Shugaban Garejin Akinyele a Jihar Oyo, Sarkin Gabas Alhaji Yaro Abubakar ya ce daga yanzu an hana yin juyen kaya da wadansu direbobin tirela ke yi da hadin kan barayi masu fashin manyan motoci. Ya ce, “Idan lalurar lalacewar mota ta taso to za mu kyale direbobin yin juyen kaya daga wata mota zuwa wata […]

An sabunta dokokin tsaron garejin Akinyele

Shugaban Garejin Akinyele a Jihar Oyo, Sarkin Gabas Alhaji Yaro Abubakar ya ce daga yanzu an hana yin juyen kaya da wadansu direbobin tirela ke yi da hadin kan barayi masu fashin manyan motoci. Ya ce, “Idan lalurar lalacewar mota ta taso to za mu kyale direbobin yin juyen kaya daga wata mota zuwa wata ne idan sun samo izini daga ofishin ’yan sanda mafi kusa.”

Aminiya ta ziyarci garejin bayan jami’an tsaro sun kama wata tirela dauke da kayan abinci na kimanin Naira miliyan 50 da aka yiwo fashinta daga Legas kwanakin baya aka yi kokarin juye kayan cikinta zuwa wata mota a cikin garejin.

Da yake karin hasken ga Aminiya kan sabunta tsaron garejin, Alhaji Yaro Abubakar ya ce, “Wannan gareji ne da ake yin dauka kaya iri-iri a tireloli da kananan motoci zuwa garuruwan Arewa kuma akwai kayan miliyoyin kudi da ke jibge cikin garejin da aka damka mana amana.

Saboda haka wajibi ne a matsayinmu na shugabanni mu dauki tsauraran matakai don tsaron lafiyar jama’a da dukiyarsu.”

Ya ce, “Akwai kyakkyawar dangantaka tsakaninmu da jami’an tsaro musamman ’yan sanda wadanda muke ba su hadin kai da hanzarta sanar da su bullar miyagun ayyuka don daukar matakan dakile su.”

Alhaji Yaro ya ce, “Saboda haka muna kira ga direbobin manya da kananan motocin sufuri da fasinjoji da kanikawa da dukkan masu ruwa-da-tsaki su taimaka wajen bayar da tasu gudunmawar tsaron garejin.”

A kwanakin baya ne garejin na Akinyele da ke kusa da birnin Ibadan ya yi kaurin suna kan yadda ’yan fashin tankokin man fetur suke cin karensu ba babbaka a dazukan da ke zagaye da garejin.

Sai dai Alhaji Yaro Abubakar ya ce, “Yanzu wannan ya zama tsohon zance domin kamar yadda na yi maka bayani tun farko akwai yaranmu da suke aikin sa-ido dare da rana wajen lura da hada- hadar motoci a ciki da wajen garejin inda suke hanzarta sanar da ’yan sanda bullar duk abin da ba mu amince da shi ba.”