An sabunta gabar ’yan kasuwar mile 12 a taron siyasa

An sabunta tsohuwar gabar da ke tsakanin shugaban kasuwar Mil 12 mai ci a yanzu, Alhaji Haruna Muhammed da daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasuwar, Alhaji Mamuda yayin da kungiyar ’yan Arewa ’yan siyasa suka yi taro don nuna goyon bayansu ga dan takarar gwamnan jihar , Akinwumi Ambode, karkashin tutar jam’iyyar APC a kwanakin […]

An sabunta gabar ’yan kasuwar mile 12 a taron siyasa
An sabunta gabar ’yan kasuwar mile 12 a taron siyasa

An sabunta tsohuwar gabar da ke tsakanin shugaban kasuwar Mil 12 mai ci a yanzu, Alhaji Haruna Muhammed da daya daga cikin tsofaffin shugabannin kasuwar, Alhaji Mamuda yayin da kungiyar ’yan Arewa ’yan siyasa suka yi taro don nuna goyon bayansu ga dan takarar gwamnan jihar , Akinwumi Ambode, karkashin tutar jam’iyyar APC a kwanakin baya.

Alhaji Haruna da Alhaji Mamuda, wadanda duk ’yan Arewa ne da ke goyon bayan jam’iyyar APC a Legas, sun dade suna kai ruwa rana dangane da shugabancin kasuwar Mil 12 a shekarun baya, inda magoya bayansu suka rika yin bata-kashi, har aka samu asarar rayuka da dukiyoyi.
Alhaji Haruna da Alhaji Mamuda, wadanda suke da goyon bayan shugabannin jam’iyyar tun daga matakin karamar hukuma, har matakin jiha sun sha zargin juna da fara tsokana da tayar da fitina, al’amarin da suka sha musantawa.
Magoya bayan Alhaji Haruna suna zargi magoya bayan Alhaji Mamuda da takalarsu da fada, inda suka yi wa magoya bayansu da dama rauni. Sai dai magoya bayan Alhaji Mamuda sun musanta zargin.
Wani wanda aka yi wa rauni, mai suna dahiru Muhammed ya bayyana cewa, lamarin ya auku yayin da suka fito daga filin taro na jam’iyyar APC.
‘Mun fito daga wurin taro mun rako shugabanmu Alhaji Haruna ya shiga mota, sai mu ma muka rika shiga mota, sai kawai muka ga mutane sun dawo a guje sai muka ga yaran Alhaji Mamuda sun taho dauke da makamai suna saran mutane, sai muka yi kokarin shiga mota sai suka tarar da mu a wurin suka rika saran mu, nan take wani ya sare ni a hannu’.
Shi ma Muhammadu Kabiru cewa ya yi ‘Mun fito daga wurin taro sai kawai na ga mutane suna gudu na waiga sai na ga yaran Mamuda rike da makamai suna saran mutane. Ni ma an yi mini rauni a baya don a lokacin da suka sare ni na ga mutane fiye da 10 da aka yi musu rauni. Kuma an ce an kashe mutum daya’.
Sai dai shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Matasan Arewa ta zaman lafiya, wato Arewa Youth Peace Forum, Alhaji Yusuf Auwal, wanda ya yi magana a madadin Alhaji Mamuda ya musanta zarge-zargen da aka yi musu, inda ya ce mutanensu ba sa wurin lokacin da lamarin ya auku.
‘Yadda suka fada ba haka ba ne. Yadda lamarin ya auku shi ne an bayar da kudi a raba, sai mutanen Alhaji Haruna suka rike kudin, suka ki bai wa sauran bangarori da suka je taron daga bisani sai fada ya kaure aka yi sare-sare a wurin. Shi ke nan sai su Alhaji Haruna suka yi mana sharri cewa mutanenmu sun yi wa mutanen su rauni. Lokacin ma mutanenmu wasu sun riga sun tafi gida, wasu kuma sun riga sun kai wurin gada a lokacin da abin ya faru. Shi kansa Alhaji Mamuda ba ya nan abin ya faru. Shi kanshi Alhaji Sani, wanda ya shiga tsakani da wasu mutanenmu biyar suna tsare a wurin jami’an tsaro. Ka san sun dade suna yi mana sharri da kiranmu ’yan boko haram ko ’yan tatsine’. Inji shi.
A cewarsa: “Lokacin da lamarin ya faru Alhaji Mamuda ba ya wurin amma sai suka yi masa sharri suke ce shi ya turo mutanensa wurin. Sun dade suna yi mana sharri Kai har karar Alhaji Mamuda suka yi cewa wai shi dan boko haram ne. Ka san abokanen adawarmu ne. Saboda haka za mu ci gaba da bin kadin hakkinmu har sai mun ga abin da ya turewa buzu nadi’.
Duk kokarin da Aminiya ta yi na jin ta bakin Alhaji Haruna ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka yi masa ba, kuma bai bayar da amsar sakon wayar da aka tura masa kan lamarin ba.
Hakazalika sakataren kasuwar da kuma magatakardar kungiyar, Alhaji Shehu Usman Samfam sun ki cewa komai kan lamarin.
Shugaban kungiyar ’yan kasuwa ’yan siyasa, wato Arewa United Political Forum kuma shugaban tawagar ’yan Arewa na jam’iyyar APC a Jihar Legas, Alhaji dandamma Yabo ya tabbatar da aukuwar lamarin.
“Gaskiya abinda ya faru ba mu ji dadinsa ba dukkanmu ’yan jam’iyyar APC ne bai kamata a ce muna fada da juna ba. Kamata ya yi mu hada kan mu, mu zauna lafiya, mu zama tsintsiya madaurinki daya mu tunkari abinda yake gabanmu don mu samu cimma nasara,’ inji shi.
Ya ce ‘sakamakon abin an yi wa mutane da dama rauni, mu ma akwai wasu mutanenmu da suka fadi a mota, sun ji ciwo mun sa an kai su gida, ana yi musu jinya har Allah ya ba su sauki’.
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce lamarin yana sashen binciken manyan laifuka da ke Panti Yaba don ci gaba da bincike.