An sabunta tsohon fim din Sholay zuwa na zamani
Shahararren fim din nan na Indiya, ‘Sholay’ wanda ya yi tashe shekaru 40 da suka gabata ya sake shiga tarihi a wannan karon, sakamakon sabunta shi da aka yi zuwa kimiyyar fim ta zamani (3D), inda aka sake shi kasuwa a Juma’ar da ta gabata.Fim din, wanda shahararrun jarumai, Amitabh Bachchan da Dharmendr da Amjad […]

Shahararren fim din nan na Indiya, ‘Sholay’ wanda ya yi tashe shekaru 40 da suka gabata ya sake shiga tarihi a wannan karon, sakamakon sabunta shi da aka yi zuwa kimiyyar fim ta zamani (3D), inda aka sake shi kasuwa a Juma’ar da ta gabata.
Fim din, wanda shahararrun jarumai, Amitabh Bachchan da Dharmendr da Amjad Khan da sauransu suka taka rawa a cikinsa, ya kasance fim din rikici da fada day a kayatar a zamaninsa. A fim din, labarin wasu barayi ne biyu da ’yan sanda suka dauka hawa da nufin su dauko musu fansa daga wani gungun ’yan fashi da makamai da suka addabi al’umma.
Kamar yadda tarihin fim din ya nuna, an fitar da shi kasuwa ne a 1975, inda aka nuna shi da farko a wani gidan silima da ke birnin Mumbai. Tun daga lokacin, sai da aka dauki tsawon shekaru biyar a jere ana nuna shi a gidajen fim daban-daban na Indiya, kafin ma a sake shi zuwa fadin duniya.
A lokacin da suke bayyana wa ’yan jarida dalilin da ya sanya suka sabunta fim din, Furodusa Shaan Uttam Singh da Sascha Sippy, sun ce sun yi haka ne domin su kayatar da ’yan zamani. Sun ce sun dauki tsawon shekara uku suna aikin sabunta fim din kuma sun kashe sama da dala miliyan uku kafin su gama.
“Daga farko, mun kwafi hotunan fim din na ainahi zuwa na’urar zamani.” Inji Singh. “Mun sabunta hotunan zuwa na zamani amma zantuttukan ’yan wasan suna nan yadda suke tun farko. Mun inganta kade-kaden da ke cikin fim din domin su dace da zamani.” Inji Sippy.
A Juma’ar da ta gabata ce aka fara nuna sabon fim din a kasar Indiya da kuma wasu sassa na kasar Hadaddar Daular Larabawa, kafim kuma a baza shi zuwa sassan duniya gaba daya a bana.
Wani kalubale da ya sarke sabon fim din na ‘Sholay’ ya kuma kusa dakile fitarsa tun da farko shi ne, yadda daraktan tsohon fim din, Ramesh Sippy ya shigar da kara kotu, yana kalubalantar hakkin mallakarsa.
Ramesh ya shigar da kara ne, inda ya kalubalanci iyalan Furodusa Sascha Sippy da sauransu, wadanda kamfanoninsu ne ke rike da hakkin mallakar tsohon fim din na ‘Sholay.’ karar tasa ba ta yi nasara ba, saboda ba ya cikin wadanda suka yi aikin sabunta fim din, don haka dole ya hakura.
Kamar yadda mai sharhi kan fina-finai, marubuci Khalid Muhammad ya ce, fim din na farko ya kasance daya daga cikin fitattu kuma ingantattun fina-finan Indiya saboda yadda Amjad Khan (ya mutu a 1992) da sauransu suka yi kokari a cikinsa.