An sace ɗaliban jami’a fiye da 20 a Benuwe

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a wannan Juma’ar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu.

An sace ɗaliban jami’a fiye da 20 a Benuwe

Fiye da ɗalibai 20 na Jami’ar Maiduguri ta Jihar Borno da na Jami’ar Jos ta Jihar Filato sun faɗa komar masu garkuwa da mutane a Jihar Benuwe.

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a wannan Juma’ar ta tabbatar da sace ɗaliban, tana mai cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Otukpo zuwa Enugu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Catherine Anene Anene ce ta sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai a birnin Makurdi.

SP Anene wadda ba ta yi wani ƙarin bayani ba, ta ce “lamarin ya faru kuma muna gudanar da bincike.”

Sai dai SP Anene ta ce waɗanda lamarin ya rutsa da su suna tafe ne a cikin wasu motocin bas biyu da misalin karfe 6.00 na yamma bayan sun ƙetare Otukpo a ranar Alhamis.

Ɗaliban jami’o’in biyu sun gamu da tsautsayin ne bayan ’yan bindigar sun tare musu hanya suna ƙoƙari ƙetarewa ta Jihar Benuwe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, fiye da ɗalibai 20 da lamarin ya rutsa da su suna karatu ne a fannin nazarin likitanci da ke kan hanyarsu ta halartar taron Ƙungiyar Ɗaliban Likitanci na shekara-shekara da za a gudanar a Jihar Enugu.