An sace Amurkawa biyu a gonar Obasanjo

An sace wasu fararen fata biyu da ake jin sun fito ne daga kasar Amurka, a wata gonar manja da aka ce mallakar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne da ke karamar Hukumar Akamkpa a Jihar Kuros Riba.Bakin Turawan biyu wasu ’yan bindiga da ba a gano ko su wane ne ba suka sace su […]

An sace Amurkawa biyu a gonar Obasanjo
An sace Amurkawa biyu a gonar Obasanjo

An sace wasu fararen fata biyu da ake jin sun fito ne daga kasar Amurka, a wata gonar manja da aka ce mallakar tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne da ke karamar Hukumar Akamkpa a Jihar Kuros Riba.
Bakin Turawan biyu wasu ’yan bindiga da ba a gano ko su wane ne ba suka sace su da karfin tsiya, kamar yadda wasu matasa da suke makwabtaka da gonar da suke zaune a kauyen Ekong Anaku da ke karamar hukumar suka bayyana.
Shaidu da ma’aikata a gonar ta Obasanjo wadanda har zuwa lokacin suke firgice sun ce, an garzaya da Turawan cikin sauri zuwa wani mazauni da ba wanda ya sani.
Lokacin da manema labari suka ziyarci kauyen a shekaranjiya Laraba bayan sun samu labarin sace Amurkawan, sun iske mutanen kauyen da dama sun gudu daga gare shi, kuma sauran wadanda suka rage a kauyen suna jin tsoron yin magana saboda irin yadda masu garkuwa da mutanen suke da karfi.
Lokacin da aka tuntube ta, majiyarmu a hedkwatar ’yan sandan jihar wadda ta roki a sakaya sunanta ta tabbatar da sace Turawan. Sai dai babu wani tabbaci kan ko an samu tuntuba a tsakanin masu garkuwa da mutanen da ’yan sanda ko wasu hukumomi ba.
Sai dai wata babbar majiya ta jami’an tsaro ta ce suna aiki wurjanjan domin gano fararen mutanen, amma ba za ta bayyana dabarun da suke bi ba, ko yin magana da manema labarai ba tukuna.
 Idan za a iya tunawa a farkon wannan wata ne, ’yan sanda suka ceto wani yaro da aka sace tare da yin garkuwa da shi a yankin Ogoja da ke jihar.
Sakamakon yadda ayyukan sacewa da yin garkuwa da mutane ke habaka a jihar ne ya sa a makon jiya lokacin da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kola Shodipo ke nuna wa manema labari wasu masu garkuwa da mutane, ya ce zai hana masu yin garkuwa da mutane da sauran miyagu yin sakat a jihar.  
Sodipo ya ce kai farmaki ga masu aikata miyagun ayyuka a Jihar Kuros Riba yana samar da sakamako mai kyau ta hanyar kama wadanda ake zargi da aikata miyagun ayyuka da kwato makamai da harsasai.