An sace dan majalisar Jihar Adamawa

An sace dan Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Alhaji Adamu Usman a gidansa da ke layin Numan a garin Yola. A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka sace Adamu Usman da yamma daga gidansa da karfi da yaji duk da iyalansa sun rika ba da hakuri ga masu sace shi.Kakakin ’Yan sandan Jihar DSP Othman […]

An sace dan majalisar Jihar Adamawa
An sace dan majalisar Jihar Adamawa

An sace dan Majalisar Dokokin Jihar Adamawa Alhaji Adamu Usman a gidansa da ke layin Numan a garin Yola.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka sace Adamu Usman da yamma daga gidansa da karfi da yaji duk da iyalansa sun rika ba da hakuri ga masu sace shi.
Kakakin ’Yan sandan Jihar DSP Othman Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce ’yan sanda na bincike a kan lamarin.
Ya shawarci jama’a su anya ido kuma in sun ga wanda suke zargi kan take-takensa a yi maza a kai kara ofishinsu da ke kusa.
dan majalisarr dai na wakiltar karamar Hukumar Toungo ne a majalisar jihar