An sace Fulani 26 cikin mako biyu a Jihar Kano

Fulani makiyaya na ci gaba da fuskantar tashin hankali sakakamon yadda ake ci gaba da sace su ana yin garkuwa da  su a kananan hukommin Doguwa da Sumaila da ke Jihar Kano.Da yake tabbatar da faruwar lamarin Shugaban kungiyar Jin dadin Fulani ta Jihar Kano (FULDAN) Alhaji Sanusi Dawakin Tofa ya ce a kasa da […]

An sace Fulani 26 cikin mako biyu a Jihar Kano
An sace Fulani 26 cikin mako biyu a Jihar Kano

Fulani makiyaya na ci gaba da fuskantar tashin hankali sakakamon yadda ake ci gaba da sace su ana yin garkuwa da  su a kananan hukommin Doguwa da Sumaila da ke Jihar Kano.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin Shugaban kungiyar Jin dadin Fulani ta Jihar Kano (FULDAN) Alhaji Sanusi Dawakin Tofa ya ce a kasa da mako biyu an sace Fulani akalla 26, wadanda har yanzu ba a sako su ba sakamon rashin biyan kudin fansa daga iyalansu.
Shugaban Fuldan din ya ce, “Masu garkuwa da mutanen sukan nemi kudin fansa daga iylan wadanda suka sace, kudin da yake gagarar biya musamman saboda yawan kudin da suke nema. Za ki ji sun nemi Naira uku ko miliyan shida da sauransu, idan ka duba wadansu da aka sace ko Naira miliyan daya ba su da ita.”
A ranar Talatar da ta gabata ma a garin Kwanduna da ke karamar Hukumar Doguwa an sace wadansu Fulani uku ciki har da wani dattojo mai shekara sama da dari mai suna Alhaji danduna. Wani dan uwan dattijon da Aminiya ta tattauna da shi ya ce masu garkuwa da mutanen sun addabe su, ya ce daga tsayawar damina an shiga gidaje sama da dari. “A yanzu haka gidaje daidai ne da masu garkuwa da mutanen ba su shiga sun dauki mutane a garinmu ba. A yau din nan (Talata) sun sace mana ’yan uwa uku da suka hada da Alhaji danduna da kanensa da babban dansa.  Iyalansu suna nan sun shiga cikin tashin hankali,” inji shi.
Aminiya ta gano cewa yin garkuwa da mutanen ya tilasta mutane da dama kaurace wa yankin don tsira da rayuwarsu. Har ila yau jama’ar kauyen sun ce ’yan sanda ba su kula da lamarinsu, saboda duk lokacin da aka sace wani ko sun sanar da ’yan sanda ba a tura musu kowa don daukar mataki a kai.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakkin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya ce sabon Kwamshinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Rabi’u Yusuf ya lashi takobin kawo karshen garkuwa da mutane a jihar.