An sace Hakimin Birnin Gwari
A Jihar Kaduna kuma a shekaranjiya Laraba an yi garkuwa da Hakimin Birnin Gwari ta Tsakiya, Alhaji Abubakar Yahaya a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, shi da wani tsohon Sakataren Ilimi a jihar, Ibrahim Musa wanda ake kira Ibrahim ES. Wata majiya a Birnin Gwari ta ce, “Duka su biyun suna tafiya tare ne a mota […]
A Jihar Kaduna kuma a shekaranjiya Laraba an yi garkuwa da Hakimin Birnin Gwari ta Tsakiya, Alhaji Abubakar Yahaya a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, shi da wani tsohon Sakataren Ilimi a jihar, Ibrahim Musa wanda ake kira Ibrahim ES.
Wata majiya a Birnin Gwari ta ce, “Duka su biyun suna tafiya tare ne a mota daya lokacin da aka sace su.”
Aminiya ta gano cewa harkokin garkuwa da mutanesun dan tsagaita a yankin saboda sulhun da ake yi a tsakanin ’yan bindigar da mutanen yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya ce zai bincika kafin ya yi karin haske.