An sace jami’in gwamnati a kusa da sansanin sojin Abuja

’Yan bindiga sun kai hari a kusa da sansanin sojojoi a Abuja, inda suka dauke wani darakta a hukumar samar da gidaje ta kasa.

An sace jami’in gwamnati a kusa da sansanin sojin Abuja

ƙofar shiga birnin tarayya Abuja

’Yan bindiga sun kai hari a kusa da sansanin sojojoi a Abuja, inda suka dauke wani darakta a hukumar samar da gidaje ta kasa.

Maharan sun kai harin ne a yankin Karamar Hukuamr Bwari inda suka dauke Mista Aondo Ver.

Cikin mutanen da ke zaune a yankin da al’amarin ya faru, akwai jami’an tsaro da ke aiki, da wadanda suka yi ritaya da dama.

A kwanakin nan Abuja  na fama da matsalar tsaro, abun da ya sa ake ta kira ga mahukunta dasu gaggauta daukar matakan magance matsalar.