An sace jariri bayan kwana uku da haihuwa

Wata mata ta tsere da jariri mai kwana uku da haihuwa daga zuwa gaisuwa a gidan mai jego.

An sace jariri bayan kwana uku da haihuwa

An sace wani jariri bayan kwana uku da haihuwarsa a Sabon Garin Unguwan Mu’azu, da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.

Ana zargin wata mata mai suna Amina ce ta yi batar dabo da jaririn bayan ta ce wa makwabta uwar jaririn ce ta goya mata shi ta je ta taya ta sayayya kafin da fito daga wanka.

Mai jegon mai suna Bilkisu a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sa da zumunta ta ce ta hadu da Amina ne a wurin awo a Asibitin Yusuf Dan Tsoho da ke unguwar Tudun Wada.

Mahifiyar jairirin wadda ta ce ta hta ce “Bayan na haihu ranar Laraba na kira ta na sanar da ita cewa na haifi namiji.

“Ranar Alhamis ta zo gidana cewa mijinta ne ya rage mata hanya sai ta karaso ta yi min barka; a nan ne ta ke gaya mini cewa dan da ta haifa ya rasu; ta zauna a wurina har bayan karfe takwas na dare.

“Washegari ta sake dawowa da misalin 7 na safe cewa mijinta ne zai tafi Abuja shi ne ya kawo ta.

“Na ce mata ba ni da madara sai ta ce bari ta je ta sayo min, sai na ba ta N1,000.

“Sai ta ce ko ta goya jaririn ta je da shi ne tunda ni zan shiga wanka saboda kada ya fado daga gado.

“Ina cikin bayi ta yi min sallama tun daga nan ban sake ganin ta ko jaririna ba kuma muna ta kiran wayanta ba ta shiga”, inji mai jegon mai suna Bilkisu.

Ta kwatanta matar da ake zargin cewa baka ce mai kiba da tsage a fuskarta kuma tana da kimanin shekaru 20.

Mai jegon mai suna Bilkisu a cikin wani bidiyo da ya karade shafukan sa da zumunta ta ce ta hadu da Amina ne a wurin awo a Asibitin Yusuf Dan Tsoho da ke unguwar Tudun Wada.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya ce Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar na ci gaba da binciken lamarin.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Tags