An sace jaririn wata 3, ana garkuwa da shi
Kama mutane a yi garkuwa da su domin neman kudin fansa da yankin Kudu maso Gabas ya yi kamari kuma ya dauki sabon salo, domin yanzu har jarirai ake kamawa, lamarin da ya sa mata masu goyo suna zama cikin firgici. Wani rahoto daga garin Aba a Jihar Abiya ya bayyana an kama wani jariri […]
Kama mutane a yi garkuwa da su domin neman kudin fansa da yankin Kudu maso Gabas ya yi kamari kuma ya dauki sabon salo, domin yanzu har jarirai ake kamawa, lamarin da ya sa mata masu goyo suna zama cikin firgici. Wani rahoto daga garin Aba a Jihar Abiya ya bayyana an kama wani jariri dan wata uku da haihuwa mai suna Testimony Chidiebube da safe a unguwar Umunba da ke yankin Osisioma, ana garkuwa da shi.
Majiyar labarin wannan jarida ta yi bayanin cewa wadanda suka zo kama yaron, bayan sun tsorata iyayensa da miyagun makamai, sai suka nufi inda yake kwance suka dauke shi suka fita, su kuma iyayen ba su nuna wani zafin kai ba dangane da al’amarin.
Wasu makwabtan iyayen yaron da suka bukaci a sakaya sunansu sun shaida wa manema labarai cewa masu garkuwar, bayan shigarsu gidan, kamar wadanda suka zo sada zumunci, ashe suna dauke da miyagun makamai a boye, sai suka fitar da su kuma suka bayyana abin da ya kawo su, su kuma iyayen Testimony ba su ce musu uffan ba, har suka dauki yaron suka fita, sannan suka sanar wa makwabta halin da ake ciki, alhali barayin sun tafi.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin mahaifin yaron, mai suna Sunday Udo ko suna tuntubar mutanen domin fansar yaron, sai ya ce ba zai iya cewa komai ba tukuna, amma dai suna kan haka kuma ga alama haka za ta cimma ruwa.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar ta Abiya, Usman Tilli Abubakar ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin, ina ya nuna jami’an rundunarsa na bakin kokari wajen ceto yaron ba tare da an yi masa ko ya sami lahani ba, daga hannun wadanda suka sace shi.