An sace katinan zabe dubu 2,045 a Akwa Ibom – INEC

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce, an sace katinan zabe dubu 2,045 a  ofishin zaben karamar hukumar Okobo da ke jihar Akwa Ibom lokacin zaben fidda gwani. Kwamishinan zabe da ke wakiltar jihohin Akwa Ibom, Delta da Kuros Riba Dakta Mohammed Lecky ya ce, yanzu haka jami’an ‘yan sanda su na binciken lamarin. Kwamishinan […]

An sace katinan zabe dubu 2,045 a Akwa Ibom – INEC

Katinan zabe

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta ce, an sace katinan zabe dubu 2,045 a  ofishin zaben karamar hukumar Okobo da ke jihar Akwa Ibom lokacin zaben fidda gwani.

Kwamishinan zabe da ke wakiltar jihohin Akwa Ibom, Delta da Kuros Riba Dakta Mohammed Lecky ya ce, yanzu haka jami’an ‘yan sanda su na binciken lamarin.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne lokacin da ake gabatar da rijistar zaben masu kada kuri’a na zaben 2019.