An sace mace mai shayarwa da danta a Neja
Maharan sun jikkata jami’an tsaro a yayin musayar wuta da suka yi a yankin Garin Gabas
An yi garkuwa da wata mata mai shayarwa tare da dan nata da take shayarwa da wani mutum guda a yankin Garin Gabas da ke Jihar Neja.
Jami’an tsaro biyu kuma sun samu raunuka a yayin musayar wuta a lokacin da yan bindiga suka kai da misalin karfe 1 na dare a kauyen da ke Karamar Hukumar Rafi ta jihar.
- Davido na shan suka kan bidiyon wakar ‘cin zarafin Musulunci’
- NAJERIYA A YAU: Me Zai Faru Idan Tinubu Bai Miƙa Sunayen Ministoci A Wannan Makon Ba?
Wani shaida ya ce, “’Yan bindiga sun harbi mutum biyu, sun sace babura biu, sannan suka kona motar jami’an tsaro da kuma wata mota, sannan suka yi awon gaba da wata mai shayarwa da danta da wani mutum daya.”
Da yake tabbatar da harin ta cikin wata sanarwa, sakataren yada labaran gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, ya bayyana harin a matsayin abin takaici.
Ya ruwaito Gwamna Ibrahim Umar Bago, yana cewa “jami’an tsaron da aka girke a makarantar firamaren Garin Gabas sun yi artabu da wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton sun koro shanun sata, inda a yayin arangamar suka sace mutum uku, jami’an tsaro biyu suka samu rauni.”
Sanarwar ta ce Gwamna Bago ya jajanta wa iyalan da abin ya shafa da kuma daukacin Masarautar Kagara game da lamarin.