An sace mahafiyar babban dan kasuwa a Jigawa

Wadansu mutane dauke da bindigogi da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hajiya Safiya mahaifiyar wani babban dan kasuwa mamallakin gidajen man fetur na Jahun Petroleum a gidanta da ke Karamar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Daya daga cikin ’ya’yanta Malam Salisu Angas ya ce abin ya faru a ranar Lahadin da […]

An sace mahafiyar babban dan kasuwa a Jigawa
An sace mahafiyar babban dan kasuwa a Jigawa

Wadansu mutane dauke da bindigogi da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hajiya Safiya mahaifiyar wani babban dan kasuwa mamallakin gidajen man fetur na Jahun Petroleum a gidanta da ke Karamar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa.

Daya daga cikin ’ya’yanta Malam Salisu Angas ya ce abin ya faru a ranar Lahadin da ta gabata da misalin karfe uku na dare, inda iyalan suka bukaci ba su kudi su kyale ta, amma suka ce ba kudi suke so ba a lokacin, suna so su tafi da ita ce.

Ya ce yanzu haka babban yayansu Alhaji Haruna Uje yana kwance a asibitin Malam Aminu Kano likitoci suna kokarin ceto ransa bayan da ya samu labarin sace mahaifiyarsu da aka yi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya ce bai samu labarin ba.