An sace mai ciki da ’yarta a Adamawa
Wadansu mutane dauke da bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don amsar kudin fansa, sun kai hari kauyen Monduba da ke Karamar Hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa, inda suka sace wata matar aure da ke dauke da ciki da kuma ’yarta mai shekara 8. Yankin dai na kusa ne da […]
Wadansu mutane dauke da bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne don amsar kudin fansa, sun kai hari kauyen Monduba da ke Karamar Hukumar Mubi ta Kudu a Jihar Adamawa, inda suka sace wata matar aure da ke dauke da ciki da kuma ’yarta mai shekara 8. Yankin dai na kusa ne da iyakar Najeriya da kasar Kamaru.
Lamarin wanda ya faru da tsakar dare a ranar Talatar da ta gabata kamar yadda Aminiya ta samu labari, bayanai sun ce maharan su 5 da farko sun kai hari ne a gidan wani jagoran al’umma a kauyen mai suna Alhaji Yusuf Monduba, inda suka je kofar dakinsa tare da sanar da shi cewa su bakinsa ne daga garin Marwa da ke kasar Kamaru.
Bayanai sun ce dattijon ya bukaci su yi hakuri su kwana a barandar dakin, kasancewar ba zai yi kasadar bude kofar dakinsa a lokacin ba, ganin cewa ba ya tsammanin zuwan wani bako. Hakan ya fusata ’yan bindigar inda nan take suka yi ta harba bindigarsu a dakin, lamarin da ya kai ga yi masa rauni a daya daga cikin kafafunsa, inda a yanzu haka yake jinya a Babban Asibitin Mubi.
Majiyar Aminiya ta ce mutanen sun koma bangaren ’ya’yan mutumin da ke hade da gidan, inda suka sace dansa. Sai dai a cewar majiyar matashin ya samu damar kubuta a lokacin da suke tafiya da shi, kuma hakan ne ya fusata su suka sake dawowa gidan dan suka sace matarsa mai juna biyu da ’yarsa mai shekara 8.
Aminiya ta samu labarin cewa ’yan bindigar sun yi waya da danginsa, “Sai dai ba su bayyana abin da suke bukata ba a matsayin kudin fansa tukun.