An sace manoma 11 a Abuja

Maharan sun sace manoman yayin da suke aiki a gonakinsua kauyen.

An sace manoma 11 a Abuja

’Yan bindiga sun sace manoma 11 a yankunan Achimbi da Gumanyi da ke Kwaku a yankin Kuje a Abuja.

Wani mazaunin Achimbi, Yunusa Aliyu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da misalin karfe 11:00 na safe lokacin da manoman suke girbin doya a gonakinsu.

Ya ce ’yan bindigar dauke da muggan makamai ba zato ba tsammani suka kewaye su, nan take suka yi awon gaba da su.

Aliyu, ya ce ’yan bindigar sun fara sace wani manomi a wata gona da ke Gumanyi kafin su wuce Achimbi su yi awon gaba da wasu 10 a can.

Ya ce ya zuwa yanzu maharan ba su tuntubi iyalan wadanda suka sace ba, domin neman kudin fansa.

Ya kara da cewa shugaban maharan ya ce ba zai yi magana game da kudin fansa ba har sai ya gana da shugaban kauyen Achimbi.

“Kuma yanzu mun rude saboda shugabansu ya ce ba zai yi magana game da kudin fansa ba har sai ya gana da shugaban kauyenmu.

“Kuma shugaban kauyen nan ya yi tafiya ba ya nan, duk da cewa ana sa ran zai dawo yau Lahadi ko Litinin,” in ji shi.

Lokacin da aka tuntubi, kakakin rundunar ’yan sandan birnin tarayya, SP Adeh Josephine, ta ce ba ta da masaniyar faruwar lamarin.

Amma ta yi alkawarin yin karin haske da zarar ta samu bayani.

An harbe ’yan sanda biyu a Yobe

Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’