An sace masa mota yana barci a ciki, bayan motar ta yi hadari ya farka

Wani mutum da ya kwanta a kujerar bayan motarsa yana barci a jihar Delaware a Amurka an sace shi da motarsa, har sai da motar ta yi hadari ya farka daga barcin, a cewarsa a hakan ya faru ne kamar mafarki. Wanda aka sace shi da motarsa wani mawaki ne mai suna Justin Koerner ya […]

An sace masa mota yana barci a ciki, bayan motar ta yi hadari ya farka

Wani mutum da ya kwanta a kujerar bayan motarsa yana barci a jihar Delaware a Amurka an sace shi da motarsa, har sai da motar ta yi hadari ya farka daga barcin, a cewarsa a hakan ya faru ne kamar mafarki.

Wanda aka sace shi da motarsa wani mawaki ne mai suna Justin Koerner ya bayyanawa kafar yada labarai ta News Journal yadda lamarin ya faru kamar haka, “Na yi dare ina ta kadade da abokaina sai naji barci, sai na shiga cikin mota, ina barci sai na yi mafarkin wani ya yi tsalle ya fado kujerar gaban motar da nake ciki.

A rahoton ‘yan sandan Newark sun ce, wani ya fito daga cikin mota da sassafe, bayan sun binciki motar sai ga wani a cikin motar yana barci a kujerar bayan motar, amma sun saki wanda ke tuka motar yayin da motar ta yi hadari.

Justin, ya ce ya farka yaga motar ba a inda ya ajiye ta saboda ta fita daga hanya ta yi cikin daji kuma ta yi mummunan hadari, daga nan ya fahimci lallai ba mafarki yake yi ba.

Justin ya kara da cewa, Jami`an `yan sanda sun yi shirin su fitar da shi daga halin da yake ciki sai wani jami’in tsaro da yake makwabtaka da wurin da hadarin ya faru ya ce, ya nada hoton bidiyon yadda lamarin ya kasance.

 

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo

China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas